Dakarun sojoji da ke karkashin Bataliyar 8 a ranar Talata sun samu nasarar hallaka ‘yan fashin daji da dama tare da kwato makamai daga hannunsu a jihar Sokoto.
A wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na sojoji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya ce, sojojin sun kaddamar da samamen ne a kauyen Tukandu, inda suka afka wa ‘yan fashin daji da suka yi kaurin suna wajen addabar jama’a da ayyukansu na ta’addanci a yankin baki daya.
- Kutsen Da Wasu Jiragen Ruwan Philippines Suka Yi A Ren’ai Jiao Dake Tekun Kudancin Kasar Sin Ya Bayyana Makircin Amurka
- An Gudanar Da Taron Manyan Jami’ai Karo Na 16 Na Dandalin FOCAC
A bisa wannan kokarin, ya ce, sojojin sun hallaka ‘yan ta’addan yayin da wasu suka tsira da raunukan harbin bindiga a jikinsu.
Bayan samamen da suka yi, sojoji sun kwato bindiga kirar AK-47 guda uku, bindiga kirar PKT, alburusai masu guda 125, bama-bamai guda biyu, da kuma mashina guda tara.
Shugaban sojojin Nijeriya, Taoreed Lagbaja, ya jinjina wa kokarin sojojin, inda ya nemi su kara himma da kwazo har zuwa lokacin da za a tabbata da kakkabe dukkanin ‘yan ta’addan da suke addabar jama’a a kasar nan.