Kotun koli ta ce ba za ta yi duba ba kan shaidar takardun karatun Shugaba Tinubu ba da ya samu a jami’ar Jihar Chicago da ke kasar Amurka wacce ya mika wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) domin tsaya wa takara a zaben shugaban kasa na 2023.
Kotun kolin ta ki amincewa da Batun Mai shigar da kara, tana mai cewa, wa’adin kwanaki 180 da kundun tsarin mulki kasa ya tanada, ba zai yi wu a ketare ba.
- Sabon Tsarin Biyan Albashi: Gwamnati Za Ta Cire Ma’aikatan Da Ba A Tantance Su Ba, Gobe
- Amurka Ce Ke Rura Wutar Rikici A Tsakanin Palasdinu Da Isra’ila
Don haka kotun koli ta ki amincewa da sabbin hujjojin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayar na soke zaben shugaba Tinubu, inda ta ce, ba za ta iya amfani da sashe na 22 ba bayan cikar kwanaki 180.
Kotun kolin ta kuma ce ba za ta iya duba batun shari’ar da ba a yi ba a kananan kotuna ba, ba kuma za ta bari a yi wa shari’ar kwaskwarima ba.
Don haka, kwamitin Alkalan Kotun Koli karkashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro, ya ce ba shi da hurumin sauraren karar Atiku Abubakar. Don haka, Kotun ta tabbatar da Nasarar Tinubu ta yi fatali da karar da Atiku da Obi suka shigar.