Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa amfani da kayan aiki na zamani a gidajen rediyo da talbijin na da muhimmanci ga gwamnatin Bola Tinubu.
Haka kuma, ya jaddada alwashin gwamnati na bai wa harkokin bunƙasa kayan aikin rediyo, talabijin da shirya fina-finai goyon baya saboda muhimmancin su ga bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
- Cin Bashi Don Aiwatar Da Kasafin Kudi Ba Sabon Abu Ba Ne A Nijeriya —Ministan Kasafin Kudi
- Tinubu Ya Sadaukar Da Kai Ga Manufofin Nijeriya Da Afrika A Duniya – Minista
Ya ce, su na a sahun gaba wajen samun nasarar inganta tattalin arziki a ƙarƙashin ajandar Farfaɗo da Martabar Nijeriya ta ‘Hope Agenda’ da gwamnatin Tinubu ta himmatu a kai.
Da ya ke jawabi wurin taron AFRICAST na 13 a ranar Talata, a otal ɗin Marriot da ke Ikeja, Legas, ministan ya nuna farin cikin sa, ganin yadda taron ya kasance ƙasaitacce, duba da yadda ya ke tafiya bisa kyakkyawan shugabanci, ake bajekolin ilmi da kuma samun damarmakin bunƙasa kasuwancin fasaha da na’urorin zamani.
Ya ce Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NBC) ta ƙirƙiro AFRICAST ne ganin yadda ake samun yawaitar kafa gidajen rediyo, talabijin da bunƙasar harkokin fina-finai da sauran kafafen sadarwa.
Idris ya yaba wa masu shirya taron, wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar NIFS, ya ce taron ya samar da wani dandalin da ƙwararru a harkokin fina-finai da talabijin za su samu dama da lasisin bayyana hajar su.
ya bayyana muhimmancin samar da shirye-shirye masu nagarta wajen nishaɗantarwa da ilmantarwa.
Ministan ya jaddada ƙoƙarin da gwamnati ke yi domin komawa amfani da tsarin DSO wajen yaɗa labarai, tare da himma wajen rungumar duk wata hanyar yaɗa labarai ta zamani da ake amfani da ita a duniya.
Ya ce Shugaba Tinubu zai kasance jagora wajen rungumar shirin amfani da na’urorin zamani a kafafen yaɗa labarai a gidajen rediyo da talabijin na Gwamnatin Tarayya.