Gwamnatin Jihar Zamfara ta fito da sabbin hujjoji na yadda tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ta yi sama da fadi da kudin aikin tashar jirgin sama.
A ranar Juma’ar da ta gabata ce Matawalle ya musanta zargin sace biliyoyin kudi da sunan aikin jirgin saman.
- Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Shenzhou-17 Dauke Da ’Yan Sama Jannati
- Sabon Tsarin Biyan Albashi: Gwamnati Za Ta Cire Ma’aikatan Da Ba A Tantance Su Ba, Gobe
A wata takardar manema labarai, wacce mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau cikin makon nan, ta ce musanta wannan batu ba komi ba ne face rashin kunya da kuma kira wa kai fallasa.
Ya kara da cewa, idan ma dai ban da Matawalle na kokarin wawitar da mutane, ya manta yadda a ranar 25 ga watan Oktoban 2021 ya kira waya ya ba da umurni aka fitar da Naira biliyan daya daga asusun Ma’aikatar Kananan Hukumomi, wanda a ciki ne aka tura wa ‘dan kwangilar aikin tashar jirgin sama Naira Miliyan 825.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Gwamnatin Jihar Zamfara ba ta yi niyyar tanka wa mutumin da ake zargi da satar dukiyar al’umma ba. Sai dai kawai don a fayyace tsakanin gaskiya da karya, musamman ma ganin cewa ya fito ya musanta zargin da ake yi masa.
“Babu makawa, satar rashin imanin da aka tafka da sunan samar da tashar jirgin sama a Zamfara ba komi ba ne idan aka kwatanta da irin manyan sace-sacen da aka tafka wa jihar da al’ummarta.
“ Tsabar karya ne a ce wai kudin da ‘yan kwangila suka gabatar da farko ya kai biliyan 28, amma aka zaftare shi zuwa biliyan 11. Babu wani dan kwangila da zai Aminta a zaftare mishi kudin aiki da kaso 61% ba tare da asalin aikin ya tabu ba. Wannan ya sa shakku a asalin aikin tun farko. Ko ba komi Matawalle ya fallasa mana nagartar dan kwangilan da suka kawo.
“Matawalle, ya yi ikirarin cewa aikin na tashar jirgin sama wai an fara shi ne kan tsarin tallafin banki na ‘Contract Financing’. Wannan abin kunya har ina? Tsarin tallafin kudi da banki ke ba dan kwangila sunanshi ‘Contract Financing Facility’, shi kuma ana kulla shi ne tsakanin dan kwangila da banki, babu ruwan gwamnati a ciki.
“Sannan batun wai kudaden da aka biya dan kwangilar, an yi bisa sahalewar ma’aikatar da ke kula da ayyuka, shi ma karya ne. Hujjojin da muke da su, kuma wadanda muka saki a yau sun tabbatar da an biya kudin ne ba tare da bin duk wata ka’ida ba.
“Ko don tarihi yana da kyau a sani cewa, an biya ‘yan kwangilan kaso 30% na aikin a matsayin biyan farko, inda aka ba su Naira Biliyan 3,465,569,736.90 daga asusun ma’aikatar kudi ta jiha a ranar 19 ga watan Yunin 2020.
“A matsayin biya na biyu, an sake tura musu Naira biliyan 2, 310, 379, 824.60 daga asusun ma’aikatar kudin jiha a ranar 19 ga watan Yuni, 2023 da sunan bashi (wanda babu wannan tsarin sam a ka’idar gudanarwa ta gwamnati). An sake tura musu Naira miliyan 825, 000, 000.00 daga asusun ma’aikatar kananan hukumomi a ranara 25 ga watan Oktoban 2021 a matsayin biya na uku.
“Haka kuma batun da Matawalle ya yi na cewa dan kwangilan ya kammala wasu ayyukan da suka hada da hanyar tafiyar jirgi, magudanan ruwa, babbar kofar shiga tashar jirgin duk karya ne. Shi ma akwai hotunan mun sake su.
“Ikirarin wai an kammala wasu daga cikin ayyukan da kaso 50% zuwa 100% ma karya ne. Ai filin tashar jirgin na nan, duk wanda ke son gani da idonsa yana iya zuwa don ganin irin barnar da Gwamnatin Matawalle ta yi.
“Hujjojin da muke da su sun tabbatar da cewa hukumomin kula da tashoshin jirgi na tarayya irin su NCAA da NAMA duk ba a shigar da su cikin lamarin ba a farko, wanda ya saba da ka’idar gudanarwa ta sashen sufurin jiragen sama. Da a ce da gaske tsohuwar gwamnatin Matawalle take, da tun a wurin fitar da tsarin aikin tashar jirgin saman za su nemi sahhalewar wadannan hukumomi.
“Muna so Matawalle ya yi wa duniya bayanin dalilin da ya sa ya biya dan kwangila zunzurutun kudi har Naira biliyan 6.78 kan aikin da su kansu sun tabbatar da cewa iyakarsa kaso 30%. Wanda kuma yanzu aka yi watsi da shi.
“Gwamnatin Dauda Lawal ba shaci fadi take fitarwa ba, hujjoji ne wadanda kowannensu ke da takarda. Kwamitin amsar mulki ya yi dogon nazari kan huldodin gwamnatin da ta gabata da kadarori da basussukan da ta bari, inda rahoton kwamitin ya bankado abubuwa masu matukar tayar da hankali.
“Da sannu za mu fitar wa da al’umma irin satar rashin imanin da gwamnatin da ta gabata ta tafka. Kuma babu ko tantama cewa duk wadanda ke da hannu a irin wadannan ayyuka na almundahana da babakere ba za su sha ba. Wannan ba komi ba ne daga cikin abubuwan takaicin da za mu fallasa wanda tsohuwar gwamnatin ta aikata.”
—SULAIMAN BALA IDRIS, shi ne Mai Taimaka Wa Gwamnan Jihar Zamfara Na Musamman A Kan Yada Labarai