A karshen makon jiya ne gwamnatin tarayya da sanar da cewa, ta samu nasarar jawo masu zuba jari daga kasashen waje inda suka zuba jarin fiye da na Dala Biliyan 2 don bunkasa bangaren samar da wutar lantarki cikin shekara 10 da suka wuce.
Sanarwa haka ta fito ne daga hukumnar samar da wutar lantarki a yankunan karkara, ta kuma kara da cewa, don tabbatar da wannan nasarar, gwamnati ta shiga yarjejeniyar tallafa wa juna da Bankin Duniya, Bankin Bunkasa Afirika, ‘Global Alliance for People and Planet’, ‘Rocky Mountain Institute’ da kuma ‘Japan International Cooperation Agency’.
- Gobe Za A Tsame Duk Ma’aikacin Tarayya Da Ba Ya Cikin Tsarin IPPIS Daga Biyan Albashi
- Da Ɗumi-ɗuminsa: Kotun Ƙoli Ta Yi Fatali Da Ƙarar Atiku Da Obi, Ta Tabbatar Da Nasarar Tinubu
Sauran kungiyoyin da hukumomin da aka shiga yarjejeniyar da su sun kuma hada da ‘Sustainable Energy for ALL’, ‘Agence Française de Débeloppement’, ‘The United Kingdom Nigeria Infrastructure Adbisory Facility’, ‘European Union’, ‘United Nations Industrial Debelopment Organisation’ sai kuma ‘Global Enbironment Facility’, da kuma ‘United States Agency for International Debelopment’.
Darakta mai kula bunkasar hukumar, Mutari Ibrahim, ya bayyana haka a takardar sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja, ya kuma kara da cewa, “Daga shekarar 2020 zuwa yau,, REA ta samu nasarar samar wa mutum Miliyan 7.5 wutar lantarki da kuma gidaje Miliyan 1.5, ta kuma samar da kananan tashoshin wutar lantarki mai karfin grid 130, da kuma tsarin ‘standalone’ har miliyan 1.3 a gidaje. Hukumar ta kuma samar da wutar lantar na kan titi mai amfani da hasken rana na tsawon kilomita 1,650, wamda hakan ya taimaka wajen samar da tsaro da bunkasaa ci gaban yankuna karkara.
“Haka kuma shirin REA ya kammala ayyuka 1,403 a karkashin kasafin kudin manyan ayyuka, inda aka samar da hasken wutan lantarki mai amfani da hasken rana, kananan tashar wutan lantarki, an kuma samar da wannan ci gaban ne ta hanyar ilimantarwa da harkar gona.
Hukumar ta kuma bayyana cewa, a shekarar 2022 a wani bangare na shirin rage talauci a kasa an samar da karin dala biliyan 4 inda aka zuba don bukasa tattalin arzikin al’umma tare da shirin rage radadin talauci da ake fama da shi.
An kuma shirya amfani da wani bangare na kudaden wajen samar da karin wutar lantarki a wurare fiye da 50,000 don karfafa harkokiin kananan kasuwanci masu amfani da wutar lantarki da suka hada da makarantu da wuraren ibada.