Kotun koli ta ce dan takarar shugaban kasa ba ya bukatar samun akalla kashi 25 na kuri’un da aka kada a babban birnin tarayya Abuja domin zama shugaban kasa.
Mai shari’a Iyang Okoro ya tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara cewa babban birnin tarayya Abuja ba shi da wani matsayi na musamman kuma shugaba Bola Tinubu baya bukatar kuri’u kashi 25 a babban birnin tarayya Abuja don lashe zaben shugaban kasa.
- Gwamnatin Tinubu Za Ta Muhimmanta Amfani Da Na’urorin Zamani A Gidajen Rediyo Da Talabijin – Minista
- Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Shenzhou-17 Dauke Da ’Yan Sama Jannati
Don haka kotun kolin ta amince da kotun daukaka kara cewa kashi 25 cikin 100 na ‘yan takarar jam’iyyar PDP da LP, Atiku Abubakar, da Peter Obi da ke ikirarin ba su dace ba.
Tuni da kotun ta tabbatar da nasarar shugaba Tinubu a matsayin halattaccen shugaban kasar Nijeriya.