Sojojin bataliya ta 159 da ke a garin Geidam a sashe na biyu na rundunar sojin hadaka ta Operation Hadin Kai, sun yi wa ‘yan ta’adda kwanton bauna, wanda hakan ya ba su nasarar kashe ‘yan ta’adda shida.Â
A cikin sanarwar da mataimakin mukaddashin darakatan hulda da jama’a na rundunar, Kaftin Muhammad Shehu ya fitar a ranar Alhamis ta ce, sojojin sun kuma kwato bindigun AK-47 biyu, babura biyu da kuma wayar hannu a lokacin fafatawar.
- WHO Da UNICEF Za Su Yi Wa ‘Yan Mata Miliyan 7.7 Rigakafin Cutar Kansar Mahaifa A Nijeriya
- Sin Da Kasashen Afirka Na Kara Yaukaka Kawance Karkashin Dandalin FOCAC
Sanarwar ta ce, sojojin sun yi nasarar ne a aikin da suka yi a ranar 25 na watan Okutubar 2023 a Kauyen Jororo na karamar hukumar Geidam a jihar Yobe.
Kazalika sanarwar ta kara da cewa, wasu daga cikin ‘yan ta’addar sun tsere yayin fafatarwar dauke da harbin albarusai a jinkinsu.
Bugu da kari, sanarwar ta ce, a wani aikin da sojin suka gudanar a ranar Alhamis a kauyukan Bajingo da Kurnawa a yankin Babbangida a karamar hukumar Tarmuwa a Yobe, sojin bataliya ta 233, sun kashe ‘yan ta’adda hudu sun kwato makamai da babura da sauransu.