Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya zargi ‘yan Nijeriya da yin tsayuwar daka wajen amsar dukkanin wani abin da aka bijiro musu da shi walau mai kyau ko akasin hakan.
Ya nuna cewa wasu abubuwan sun bayyana wa ‘yan Nijeriya a zahirance, amma kuma suna ci gaba da rungumar abubuwa yadda suka zo a maimakon yin abin da ya dace.
- Tun Ina Yarinya Ba Na So Na Ga Ana Zaman Banza -Rukayya Usman
- CMG Da IOC Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Hadin Gwiwa
Amaechi, wanda ya shiga harkokin siyasa a 1999 zuwa 2023, wanda ke magana a matsayin babban bako a taron lakca na shekara-shekara na TheNiche wanda ya gudana a cibiyar NIIA da ke Victoria Island a jihar Legas ranar Alhamis.
Duk da cewa an riga an bada rahoton abubuwan da suka wakana a wajen taron, sai dai a halin yanzu wani bidiyo mai tsawon mintina hudu na ci gaba da karade yanar gizo da ke kara daukar hankali.
A bidiyon, tsohon kakakin jihar Ribas kuma gwamnan jihar har sau biyu, ya bayar da dalilan da suka sanya ya yi gum da bakinsa, daga cikin dalilan har da cewa hadiminsa a bangaren yada labarai ya shawarcesa da ya yi shiru.
“Akwai gidajen talabijin da daidaikun da suka yi ta samu na da cewa na yi magana kan batutuwa daban-daban tun lokacin da na bar ofis, amma na ki amincewa na yi maganar. Na ki yin hakan ne bisa dalilai guda biyu, na daya hadimina a bangaren yada labarai ya shawarce ni da kada na ce komai, ya fusata sosai da nake magana da ku.
“Na biyu, ‘yan Nijeriya ba su mayar da hankali kan komai ba. Abu saboda kawai da za a ce, ‘yan Nijeriya ba su kula kan komai, suna rungumar komai yadda ya zo musu. Akwai wani dan siyasa da ya taba ce muku shi ba barawo ba ne? wani dan siyasa ne ya halarci jami’a? wacce ‘yar siyasa ce ta ce muku ta yi hidimar kasa NYSC, sannan wani dan siyasa ne ya gaya muku yana da satifiket?”
Ya kara da nuni da cewa, duk da ‘yan Nijeriya sun san wasu ‘yan siyasar da ba su dace ba, amma har yanzu suna ci gaba da ba su dama.
“’Yan Nijeriya sun sani amma har yanzu suna ci gaba da zabarsu, don haka menene matsayarku? Don me ma zan yi magana alhali ba wani abu ne sabo ba? ‘yan Nijeriya su ne ke da damar zabin wanda suka aminta da wanda ba su gamsu da ba, ‘yan Nijeriya ke zaban wadanda za su zaba da wadanda ba za su zaba ba. Kai, koda ka je gidan dan Nijeriya ka kashe mahaifiyarsa, babbansa zai ci gaba da harkokin rayuwarsa. Babu wani abun da zai dameka, babu fa, don haka menene zai sa na tsaya bata lokacina?”
Tsohon ministan ya ce tun lokacin gwamnatin Jonathan zuwa ta Buhari an yi ta tafka muhawara da zuba maganganu sosai amma duk da haka jiya-i-yau don haka ne ya zabi ya zauna cikin gida ya ja bakinsa ya yi shiru kawai.
Ministan ya kara da cewa ‘yan Nijeriya ba su son gaskiya, har ma ya buga misali da cewa koda mutum ya fito ya ce musu shi karya yake musu ko kuma ya tafka wani laifin amma za su cigaba da amincewa da shi koda kuwa ya ma je gidan yari ya fito.