Akalla mutane 20 ne suka mutu bayan da wani babur ya taka wani bam da ‘yan ta’addan Boko Haram suka dasa a jihar Yobe a yammacin ranar Talata.
Bam din ya tashi ne da misalin karfe 6:30 na yamma a kauyen Goni Mittiri da ke garin Gumsa a karamar hukumar Gaidam a jihar, kamar yadda shaidun gani da ido suka shaida wa LEADERSHIP.
- Tattalin Arzikin Kasashen Afirka Zai Dade Bai Farfado Ba – AFDB
- Hatsarin Kwale-Kwale: Har Yanzu Ana Neman Mutane Sama Da 70 A Taraba – NEMA
Wadanda lamarin ya rutsa da su, an ruwaito suna kan hanyarsu ta dawowa daga makabarta ne, bayan birne mutane 17 da Boko Haram suka kashe a safiyar ranar Litinin.
Wasu majiyoyi sun ce an dasa bam din ne a gefen hanya.
Daya daga cikin mazauna yankin ya ce, “Mun kidaya jimillar mutane 20 a wurin da lamarin ya faru, za mu yi jana’izar mutum 11 a wannan dare (ranar Talata).
“Sauran mutane tara da suka mutu za a birne su a gobe Laraba da karfe 9 na safe sai kuma wasu ma’aurata wadanda suke karbar magani a asibiti saboda raunukan da suka samu sakamakon fashewar bam din.”