Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce dukkanin ministocinsa, za su ci gaba da zama a ofis ne kawai bisa la’akari da ayyukan da suka yi, wanda za a rika bita lokaci zuwa lokaci.
Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bude taron majalisar ministoci da masu taimaka wa shugaban kasa da kuma manyan sakatarorin ma’aikatu na shekarar 2023, wanda ake gudana a Abuja.
- Bam Ya Yi Ajalin Mutane 20, Ya Jikkata 2 A Yobe
- Yanzu-yanzu: ‘Yansanda Sun Cafke Shugaban NLC, Joe Ajaero A Imo
“Idan kana aikinka, babu wani abin jin tsoro, amma idan ka kasa cimma manufarmu a yayin bita, tafiya zaka yi don kar ka zame wa ci gaban Nijeriya karfen kafa”
A cewar Kamfanin Dillanin Labaran Nijeriya (NAN), shugaban ya tunasar da ministocin ayyukan da ke gabansu na sauke nauyin al’ummar da ke kansu.
Ya kuma bukaci ministocin su mayar da hankali wajen samar da ci gaba a ma’aikatun da suke jagoranta, inda ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ganin ta kasance kan gaba wajen ci gaba.
Dukkanin ministocin Nijeriya sun samu halartar taron na kwana uku, in ban da ministan yawon shakatawa Misis Lola Ade-John.
A baya Tinubu ya yi irin wannan gargadi ga duk masu madafun iko a gwamnatin tasa, cewar ko dai mutum ya yi abin da ya dace ko ya ajiye aiki.