Jami’an ‘yansanda a jihar Bauchi sun yi musayar wuta da masu garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Toro, inda suka hallaka ɗan garkuwa da mutane da ceto mutum shida da aka yi garkuwa da su ciki har da wata budurwa ‘yar shekara 17, Rashida Hamisu daga maɓoyar ‘yan fashin dajin.
A ranar 1 ga watan Nuwamban 2023 ne jami’an ‘yansandan da haɗin guiwar Sauran Hukumomin tsaro (JTF) da mafarauta suka samu wani rahoton sirri kan maɓoyar masu garkuwa da mutanen da ke dazuka biyu da aka gano a Angwari da Sara.
- Sojoji Sun Kashe Dan Bindiga, Sun Kama Barayin Mota 3 A Bauchi
- Sojoji Sun Kashe Kasurgumin Kwamandan ‘Yan Bindiga A Kebbi
A sanarwar da kakakin hukumar ‘yansanda na jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ranar Alhamis, ya ce, tawagar sun yi musayar wuta da ‘yan ta’addan inda aka yi nasarar tarwatsasu tare da kashe daya daga cikinsu.
Ya ce, an kwashi waɗanda aka ceto zuwa babban asibitin Toro domin duba lafiyarsu sannan a hada su da iyalansu cikin koshin lafiya.
Kazalika, ‘yansandan sun kuma samu wani rahoton da ke cewa, wasu ‘yan bindiga sun farmaki direban hukumar kula da inganci kayayyaki (SON) da ke Bauchi tare da sace motar hukumar ƙirar Toyota Hilux Bus.
A cewarsa, ‘yansandan sun ci karo da motar a kan hanyar Maidugiri inda suka kamota zuwa cikin garin Bauchi.