Majalisar wakilai ta nemi gwamnatin tarayya ta yi gwanjon harkokin tafiyar tare da gudanar da hukumar jirgin kasan Nijeriya (NRC).
Kiran ya biyo bayan amincewa da kudurin da Dan Majalsia Sada Soli Jibia mai wakiltar mazabar Jibiya a jam’iyyar APC ta jihar Katsina, a zaman majalisar ranar Alhami na makon jiha.
- Yadda Rakiyar Gwamnan Kano Ga Tagwayen da ke Manne Da Juna Ta Dauki Hankalin Al’umma
- Mutum Miliyan 2 Za Su Ci Gajiyar Tallafin Kiwon Lafiya A Bauchi
Da yake gabatar da kudurin, ya bayyana cewa, “Bangaren harkokin jiragen kasar Nijeriya na samar da ayyukan yi ga dimbin matasa yana kuma taimaka bunkasar tattalin arzikin kasa.”
Ya ce, duk da dimbin jari da ake zubawa a bangaren, ayyukan hukumar jiragen kasa sai kara tabarbarewa yake yi, musamman in aka kwatantasu da takwarorinsu na sauran bangaren tattalin arzikin kasa.
Ya kuma yi korafin cewa, gwamnatocin da suka gabata sun kasa samar da hukumar jiragen kasa mai inganci da Nijeriya za ta yi alfahari da ita.
Dan majalisar ya kuma ce, rashin ci gaba a harkokin jiragen kasan Nijeriya ya taimaka wajen tabarbarewa hanyoyin kasar nan wanda hakan yake jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma a kullun garin Allah ya waye.
A kan haka ya nemi ta gaggauta sayar da dukkan harkokin gudanarwar jiragen kasan Nijeriya ga ‘yan kasuwan da kamfanoni masu zaman kansu, kuma al’umma da dama a kasar nan sun amince da yin haka.
Ya kuma lura da cewa, sayar da harkokin tafiyar da jiragen kasa abu ne da ya karbu a sassan duniya, musamman ganin yin haka zai kai ga samar da tsaftaccen harkar jiragen kasa zai kuma samar da ayyukan yi ga matasa zai kuma rage cin hanci da rashawa.
A kan haka majalisar ta umarci gwamnatin tarayya ta hada hannu da kwamitin majalisar a kan hakokin sufuri su don shirya yadda za a cimma wannan burin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp