Bayan kotun koli ta tabbatar da nasarar zaben Bola Ahmed Tinubu a matsayin zababben shugaban Nijeriya, yanzu lokaci ya yi da shugaban kasar zai mayar da hankali wajen inganta gwamnatinsa ta yadda zai iya tunkarar matsaloli da ke fuskantar Nijeriya kamar yadda ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabe.
Kwanaki sama da 50 kenan da kotun sauraron karar zaben shugaban kasa ta goyi bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a kan ayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu shi ya yi nasara a zaben da ya gudana a ranar 25 ga Fabrairun 2023. Yayin da ita ma kotun koli a ranar Alhamis, 26 ga Oktoba ta tabbatar da wannan hukunci.
- Baje Kolin CIIE Na Kara Jan Hankalin Sassa Kasa Da Kasa
- Sojoji Sun Kashe Kasurgumin Kwamandan ‘Yan Bindiga A Kebbi
A hukuncin, alkalan kotun kolin su bakwai sun bayyana cewa wadanda suka shigar da kara sun gaza kawo kararan hujjoji da za su kore nasarar da Tinubu ya samu a zaben shugaban kasar.
Bayan watsi da kararrakin guda biyu da ‘yan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da na LP, Mista Peter Obi suka shigar, kotun kolin ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron karar zaben shugaban kasa ta yanke a ranar 6 ga watan Satumba, inda ta tabbatar da ayyana Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya.
Hukuncin da kotun koli ta yanke, ba wai kawai ya kawo karshen duk wasu kararraki da suka shafi zaben shugaban kasa ba, har ma da tabbatar da aikin shugaban kasa na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Ayyukan sun hada da samar da ingantacciyar shugabanci, samar da ingantacciyar rayuwa ga ‘yan Nijeriya wanda hakan ta sa aka cire tallafin man fetur da kuma dawo da darajar naira, wanda gwamnatin Tinubu ta fara tun daga farkon lamari.
Sai dai babban kalubalen da ke fuskantar ‘yan Nijeriya sun hada da rashin zaman lafiya, rashin samun ci gaba, ayyukan ‘yan bindiga da kuma cin hanci da rashawa.
Kamar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ke cewa, “idan ba mu yaki ci hanci da rashawa ba, to zai kashe mu “. Cin hanci da rashawa kamar wutar daji ce da ke cin zukatan ‘yan Nijeriya. Babu wani bangare na rayuwar ‘yan Nijeriya da cin hanci bai dabaibaye ba.
Domin haka, dole ne gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali wajen karfafa yaki da cin hanci da rashawa. A lokacin yakin neman zabe, Tinubu ya yi wa ‘yan Nijeriya alkawarin sake farfado da darajar Nijeriya.
Lallai idan har ‘yan Nijeriya za su ga sauyi, to dole ne Tinubu ya tashi tsaye wajen inganta gwamnatinsa da kuma yaki da cin hanci da rashawa a kowani bangare. Mafi yawancin mutane sun yi kara ga shugaban kasa ya yi kokarin gudanar da shugabanci nagari ta yadda zai iya farfado da darajar Nijeriya a idon duniya.