Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya karbo wa jihar kayan tallafi domin raba wa wadanda rikicin ‘yan bindiga ya shafa a jihar.
Gwamnan ya ziyarci hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure ne a ranar Alhamis.
- Majalisar Wakilai Ta Nemi A Cefanar Da Sufurin Jirgin Kasa
- Dakarun Tsaron Hadin Guiwa Sun Dakile Harin ‘Yan Ta’adda Da Cafke Mutum 2 A Kano
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce sun kai ziyarar ne domin fadakarwa, duba da irin rawar da hukumar ke takawa wajen bayar da agaji ga wadanda lamarin ya shafa.
A cewarsa, Gwamnan ya samu tarba daga Tijjani Aliyu Ahmed, kwamishinan tarayya na hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure.
Ya ce: “Makasudin ziyarar Gwamna Lawal ga Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Kasa ita ce duba karin hanyoyin da za a taimaka wa wadanda harin ‘yan fashin daji suka shafa a Jihar Zamfara.
“A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya roki hukumar da ta bai wa Zamfara fifiko saboda rashin tsaro da ake fama da shi da kuma bukatar agaji.
“Gwamnan ya jaddada bukatar hadin gwiwa wajen rage wa ’yan gudun hijira radadin yanayin da suke ciki su sama da 2000 a Zamfara.”
A lokacin da yake jawabi, kwamishinan hukumar, Tijjani Aliyu Ahmed, ya jaddada aniyar hukumar na ci gaba da tallafa wa jama’ar jihar Zamfara da sauran jihohin da ke fama da matsalar rashin tsaro.
Kwamishinan ya yaba wa Gwamnan Zamfara bisa kasancewarsa shugaba na farko da ya ziyarci hukumar tun bayan hawansa mulki.
“Abin alfahari ne da kuka ziyarce mu, wanda hakan ke nuna jajircewarku wajen kyautata rayuwar jama’arku. Mun saurari bukatarku. Don haka hukumar za ta tabbatar da cewar ta yi abin da ya dace.”
Hukumar ta bayar da tallafi ga jihar Zamfara a wani bangare na aikin agajin gaggawa wanda ya hada da buhunan shinkafa, katon din taliya, kayan aikin noma na manoma, kwamfutoci, injin dinki na masana’antu, injinan yanka katako, litattafai da sauran abubuwa.