An haifi Abdulrahman Ado-Ibrahim ranar 7 ga Fabrairu 1929 shi ne Sarki na hudu na Sarautar gargajiya ta Ohinoyi ta Ebiraland mai hedikwata a Okene,Jihar Kogi na dan Attah na biyu ne yanzu “Ohinoyi”) na Ebiraland, Ibrahim Onoruoiza na gidan Sarautar Omadibi da ya yi mulki daga shekarar 1917 zuwa 1954.An nada Ado-Ibrahim a matsayin Ohinoyi na masarautar Ebira shekarar 1997 haka ya yi ta mulki har zuwa ranar lahari 29 Oktoba 2023 ya yi shekara 26 kafin rasuwar shi. Kafin a nada shi a mukamin Sarauta dan kasuwa ne wanda ya shahara wanda yawancin rayuwarsa ya zauna ne a Legas.Ado Ibrahim dan mai martaba,Alhaji Ibrahim Onoruoiza Attah da Hajiya Hauwawu Ozianuba.
Matashi Ado Ibrahim ya kammala makarantar gwaji data karatun Alkur’ani yana da shekara 11 years Daga na sai makaranatar Okene ta mulkin turawa daga shekarar 1934 zuwa 1940 saboda karunsa na Elimantare bayan ya kammla ta sai sai ya wuce zuwa Okenen.Bayan ya kamala a 0kene a 1941.Bayan yayi shekara biyu sai ya wuce shahararriyar makarantar Ondo Boys High School saboda ilimin Sakandare daga 1943 zuwa 1946.Daga 1947 – 1949 ,ya tafi kwalejin Oduduwa inda ya kammala karatun shi na Sakandare.
- Ina Da Kwarewar Shugabancin Majalisa Fiye Da Akpabio – Ndume
- Yadda Matata Ta Rasu A Kokarin Kare Mutuncinta Daga Masu Garkuwa – Yusuf
Kamfanin United African Company (UAC) ya dauke shi aiki a 1950 matsayin sabon shiga na irin aikin Shugabannin kamfanin, da ya samu kwarewa a bangaren al’amuran kudi da sayar da kaya a shekara ta 1952 sai aka kara ma shi girma aka mai da shi Kaduna a matsayin Manaja a Kamfanin Kingsway Stores, na Kaduna.
A Janairu 1953 sai ya ajiye aiki inda ya je Jos a matsayin Jami’i mai kula da harkokin ma’aikata a kamfanin Amalgamated Tin Mines na Njeriya a matsayin wanda ke sa ido akan yadda ayyuka suke tafiya a garuruwan Bukuru da Barkin Ladi.Duk a cikin shekarar ya yi makaranta ta farko data shafi al’amarin hakar ma’adinai a Jos inda hakan ne ya sa ya samu kwarewar da ta bashi damar samun mukamin Manaja.
A cikin shekarar sai Kamfanin ya tura shi kasar Afirka ta Kudu domin ya halarci wani kwas da ya shafi fasaha,wanda kamfaninin hadin gwiwa kan harkar ma’adinai.
Bayan ya dawo ne sai aka yi ma shi karin girma da mukamin Manajan sashe inda aka bas hi wani aiki dangane da tono ma’adinan Lead/Zinc Ore da suke a Izom a garin Hakimi na Abuja,da kuma jagoranta tawagar neman gwal da base a wurin.
Kafin ya kai ga samun karin matsayin ya yi rajista a matsayin dan makarantar da ba cikin makaranta yake ba domin karatun digiri a makarantar tattalin arziki ta Landan,ya kuma yi amfani ne da kayan da za su taimaka masa da kayan da aka samar a dakin karatu na na kulawar cibiyar karatu ta Ingila a Jos.
Ya hada aikin shi da ya shafi harkar ma’adinai da karatun da yake yi wanda har ya samu takardar digiri akan kididdiga daga makarantar tattalin arziki ta Ingila a shekarar 1954.
A shekarar 1955 ya samu damar karo karatu ta hanyar gidauniyar Ford ya samu tafiya kwas na wata shida kan al’amarin da ya shafi harkar talla da kasuwanci a makarantar kasuwanci ta jami’ar Harbad .
Za mu ci gaba makon gobe