Firaiministan Habasha, Abiy Ahmed, ya ba Jama’ar kasarsa haƙuri a madadin gwamnatinsa, kan gaza kare rayukansu, a rikicin baya-bayan nan da ya bulla a ƙasar.
BBC ta rawaito cewa, an kashe ɗaruruwan mutane cikin ‘yan makonnin nan, akasari a Oromia a lokacin hare-haren da gwamnati ta dora alhakinsu a kan wata kungiyar ‘yan tawaye da aka fi sani da OLA.
- Firaministan Ingila, Boris Johnson Ya Yi Murabus
- Burtaniya Ta Dau Zafi: Fiye Da Jami’ai 50 Na Firaminista Sun Yi Murabus
Kungiyar dai ta musanta zarge-zargen kuma ta zargi dakarun da ke goyon bayan gwamnati.
A majalisar dokokin kasar, ‘yan majalisar sun tambayi Mista Abiy dalilin da ya sa jami’an tsaro suka kasa hana kai hare-hare akai-akai.
Mista Abiy ya ce gwamnati na yin kokari sosai don tabbatar da tsaron lafiyar jama’a.