Wata babbar kotu da ke zamanta a birnin Legas, ta yanke wa wani matukin jirgin ruwa mai zaman kansa, Elebiju Happiness, hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari, bayan samunsa da laifin haddasa mutuwar fasinjoji 12.
BBC ta rawaito cewa, Mai shari’a Josephine Oyefeso, ta ce an samu Happiness da aikata laifuka 11 da aka zarge shi da aikatawa, ciki har da na kisan ɗan adam.
- Kotu Ta Wa Malamin Islamiyyan Da Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 8 Fyade Daurin Rai Da Rai
- Kotu Ta Yi Masa Daurin Rai-da-rai Bisa Yi Wa Tsohuwa Mai Shekara 85 Fyade
Tun da farko ƴan sandan sun shaida wa kotun cewa mutumin ya ɗebo fasinjojin ne a ranar 29 ga watan Yuli, daga Kirirkiri zuwa.
Talla
An ce ya yi ta tukin ganganci har ta kaiga lamarin da aka kama shi da aikatawa ya auku.
Talla