Gwamnatin tarayya na hasashen samun naira tiriliyan 45 daga harajin VAT a 2026, yayin da take tsammanin samun naira tiriliyan 35 a shekarar 2024, sannan ta samu naira tiriliyan 40 a shekarar 2025.
Wannan na kunshe ne a cikin kundin tsarin harajin kudade da ake tsammanin samu na gajeren zango a tsakanin 2024 zuwa 2026 na gwamnatin tarayya.
- INEC Ta Dakatar Da Zabe A Wasu Sassan Jihar Kogi
- An Yi Taron Karawa Juna Sani Tsakanin Sin Da Amurka Kan Shari’a Da Hakkin Dan Adam
A cikin kundin da Shugaba Kasa, Bola Tinubu ya tura wa majalisar kasa a makon da ya gabata kan adadin yawan kudaden da ake tsammanin samu daga bangaren harajin na BAT da ake amsa. Ana kyautata zaton cewa kudaden harajin VAT zai karu daga matsakaita na naira tiriliyan 35 a shekarar 2024, zuwa naira tiriliyan 40 a shekarar 2025 da kuma naira tiriliyan 45 a shekarar 2026, bayan daidaita lamarin a tsakanin kamfanonin da ke samar da kayayyaki.
Harajin VAT yana da matukar taka muhimmiyar yawa a cikin kudaden shiga da gwamnatin tarayya ke samu. A dai yi tsammanin shirin harajin VAT na gajeran zango zai samar da karin kashi 7.5 idan har gwamnati ta ci gaba da sabunta shi har ya kai dogon zango.
Bugu da kari, a bisa hasashen harajin da ake samu a bangaren kudin shiga wanda bai shafi fannin mai ba, kundin ya ce, duba ga raguwar da ake samu na kudaden shiga a fannin danyen mai, gwamnatin tarayya ta ci gaba da wanzar da sauye-sauye da daukar matakai don kara fadada samar da kudaden shigarta da kuma sabunta tsarin biyan haraji ta hanyar amfani da fasahar zamani.
A bangaren kudaden shiga da hukumar kwastam ke tara wa gwamnatin kuwa, sun hada da biyan kudaden fiton kaya da biyan haraji na musamman, gwamnatin ta yi tsimmayi tara kudaden harajin mai matukar yawan gaske.