ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NIS Ta Tabbatar Da Mutuwar Jami’anta 4, 7 Sun Ji Rauni A Wani Hadarin Mota A Kano

by yahuzajere
2 years ago
NIS

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) ta tabbatar da cewa jami’anta 4 sun mutu yayin da wasu 7 suka ji raunuka a wani hadarin mota da ya rusa da su a Jihar Kano.

Mai magana da yawun hukumar, DCI Adedotun Aridegbe ya bayyana haka a shalkwatar hukumar a wani taron manema labarai da ya kira yau Litinin.

Ya yi bayanin cewa, “A jiya ne wasu ma’aikatanmu goma sha daya ke dawowa Abuja daga wani aiki a Kano, a cikin wata motar bas mai daukar kujeru goma sha takwas suka yi wani mumunar hatsari, a wani wuri ‘yan kilomitoci kadan daga Kano. Sakamakon haka, ma’aikatanmu hudu sun mutu rayukansu. Wannan lokaci ne na jimami a Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya.

ADVERTISEMENT

“Abokan aikinmu guda bakwai da suka samu raunuka daban-daban a halin yanzu suna karbar magani a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Kano. Muna musu addu’ar samun lafiya cikin gaggawa.

Hukumar ta bayyana cewa, ta sanar da iyalan jami’an da abin ya shafa kafin ta kira taron manema labarai don bayyana wa duniya asalin abin da ya faru, inda yanzu haka ake shirin yi wa wadanda suka mutu jana’iza ta bangirma.

LABARAI MASU NASABA

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

“Mukaddashiyar Kwanturola Janar ta Hukumar Kula da Shige da Fice, Caroline Wura-Ola Adepoju, ta yi matukar bakin ciki da wannan rashi, kuma da kanta ta mika ta’aziyya ga iyalan mamata tare da nanata cewa hukumar tana tare da iyalan magidantan da suka mutu cikin tallafawa a wannan lokaci na alhini.” In ji shi.

Adedotun ya kuma ce, tuni Mukaddashiyar Kwanturola Janar ta ba da umarnin gudanar da bincike nan take don gano musabbabin hadarin. Kana ta sha alwashin daukar matakan da suka dace don hana faruwar hakan nan gaba.

“Wannan lokaci ne na jimami a tsakanin daukacin iyalan Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya. Mukaddashiyar CGI ta umurci dukkan ofisoshi da rassan hukumar su sassauta tutocinsu na tsawon kwanaki bakwai masu zuwa. Za mu kuma yi zaman makoki na kwanaki uku don girmamawa da tunawa da abokan aikinmu da suka mutu.” In mai magana da yawun hukumar.

  • ‘Yansanda Sun Dakile Harin ‘Yan Ta’adda, Sun Ceto Mutum 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa
Labarai

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli
Labarai

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Kotu Da Ɗansanda

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Next Post
Firaministan Pakistan Kakar: Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Tana Girmama Bambance-bambance A Tsakanin Kasa Da Kasa

Firaministan Pakistan Kakar: Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Tana Girmama Bambance-bambance A Tsakanin Kasa Da Kasa

LABARAI MASU NASABA

Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.