Dakarun rundunar Operation Whirl Punch sun kashe ‘yan ta’adda tare da kwato makamai da alburusai.
A wata sanarwa da mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin, Laftanar Kanar Musa Yahaya, ya fitar ya bayyana lamarin ya faru ne yankin dajin Maro – Chibiya a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
- Ana Sa Ran Tattalin Arzikin Kasar Sin Zai Ci Gaba Da Farfadowa A Cikin Rubu’i Na Hudu
- Majalisa Za Ta Binciki Soke Bizar ‘Yan Nijeriya 264 Da Saudiyya Ta Yi
Sojojin sun yi arangama da ‘yan ta’addan inda suka kashe daya daga cikinsu.
Ya ce a yayin farmakin sojojin sun yi artabu da ‘yan bindigar.
Ya kara da cewa sojojin sun kwato bindiga kirar AK47 guda daya, harsashi hudu da kuma wayar hannu daya.
Kazalika, a ranar 10 ga watan Nuwamba 2023, ya ce sojojin a wani aikin share fage a kauyukan Kawara da Filin Jalo da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, sun yi artabu da ‘yan bindiga a dajin Kawara.
A arangamar da suka yi, sojojin sun yi nasarar kashe dan bindiga guda daya tare da kwato bindiga kirar AK47 guda daya.
Kazalika sojojin rundunar sun gudanar da aikin share fage a kauyukan Mai-Kulu-Gwanda, Rafin Gora, Funtua Badadi da Kabawa duk a cikin karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
A yayin aikin, sojojin sun kashe dan bindiga guda daya tare da kwato babur guda daya.
Har wa yau, sun sake kashe wasu mahara guda biyu sannan suka raunata wasu da dama.
A halin da ake ciki, babban kwamandan runduna ta 1 na rundunar Operation WHIRL PUNCH, Manjo Janar Valentine Okoro, ya yaba wa dakarun wajen nuna bajintar da suka yi.