Kungiyar mahaddata Alkurani (Huffazul Kur’an) ta kasa reshen Jihar Neja, ta tallafa wa Almajirai 80 da kayan sana’o’in hannu na sama da dubu dari hudu da tamanin.
Da yake jawabi a fadarsa, Mai Martaba Sarkin Minna, Dakta Umar Faruk Bahago ya jawo hankalin masu hannu da shuni da su rika ba da tallafi a bangaren addini, musamman ganin halin da kasar ta samu kanta na rashin tsaro.
Ya ce wannan shirin na wannan kungiya abin a yaba ne musamman ganin yau an kaddamar da shirin farko na karfafa gwiwar Almajirai wajen dogaro da kai, hakan zai taimaka wa shirin gwamnati na haramta yawon barace-baracen.
Dakta Faruk ya ce lokaci yayi da iyayen yara ya kamata idan za su kai ‘ya’yansu makarantun allo su rika samar musu da abubuwan dogaro da kai ba su dogara da bara ba wajen gudanar da rayuwarsu na neman ilimin addini.