Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ko kaɗan ba ta sauya sakamakon zaɓen da ta dora a Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe (IReV) ba.
INEC ta ce, ta lura da wasu rahotanni da ta riƙa cin karo da su a kafafen yaɗa labarai, inda ake zargin ta da hargitsa sakamakon zaɓen da ta tura a manhajar IReV, na zaɓen gwamnan Jihar Kogi.
- Kotun Daukaka Kara Za Ta Sanar Da Ranar Yanke Hukunci Kan Karar Da Gwamna Sule Ya Shigar
- Ribadu Ya Bukaci NLC Ta Janye Yajin Aiki, Ya Yi Allah Wadai Da Cin Zarafin Da Aka Yi Wa Ajaero
Kogi na ɗaya daga cikin jihohi uku da aka yi zaɓen gwamna a ranar 11 ga Nuwamba. Sauran jihohin biyu su ne Imo da kuma Bayelsa.
Cikin sanarwar da INEC ta fitar a ranar Talata, ta ja hankulan jama’a cewa, su yi watsi da zargin cewa, hukumar ta sauya sakamakon zaɓen da ta dora a manhajar IReV.
Ta bayyana cewa wannan zargi da aka yi wa hukumar “ƙage ne kawai domin tada hankulan jama’a.”
Wannan kakkausan martani na INEC na ƙunshe cikin wata sanarwar da Kwamishinan Tarayya na hukumar, Mohammed Haruna ya fitar a ranar Talata.
INEC ta ce babu inda ta sauya sakamakon zaɓe don a zalinci wani ɗan takara ko a fifita wani ɗan takarar kan wani.
Hukumar ta ce dukkan sakamakon zaɓen da aka gani a jihohin uku, shi ne abin da jama’a suka zaɓa, kuma shi ne INEC ɗin ta bayyana.
Idan ba a manta ba, tun a ranar zaɓe INEC ta fito ƙarara kamar yadda ta saba yi a kowane zaɓe, cewa ba ta da ɗan takarar ko ɗaya. Ɗan takara a cewar ta, na jam’iyya ne da ‘yan jam’iyya. Don haka sai wanda jama’a suka zaɓa.
Aikin INEC inji hukumar shi ne shirya zaɓe sahihi kuma karɓaɓɓe, kamar yadda a kowane lokaci a ke yin bakin ƙoƙarinta.