• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Akwai Kyakkyawan Fata Game Da Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka A Wannan Karo

by CGTN Hausa
2 years ago
sin

Ga duk mai bibiyar muhimman harkokin dake gudana a ’yan kwanakin nan, ba zai gaza lura da yadda hankula suka karkata ga ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping yake yi a kasar Amurka ba, duba da yadda wannan ziyara ta yi matukar jan hankulan sassan kasa da kasa, inda tuni shugaba Xi ya gana kai tsaye tare da takwaransa na Amurka, kuma mai masaukinsa Joe Biden, a katafaren gidan alfarman nan na Filoli dake birnin San Francisco, ganawar ido da ido da ta kasance ta farko tsakanin shugabannin biyu, tun bayan haduwarsu a tsibirin Bali na  Indonesia a shekarar bara.

Bayan tattaunawa tsakanin shugabannin biyu game da muhimman batutuwa, da musayar ra’ayoyi kan abubuwan dake matukar jan hankulan kasashensu, musamman wadanda suka jibanci yadda za a farfado, da kara kyautata dangantakar Sin da Amurka, da ma batutuwan dake shafar zaman lafiya da ci gaban duniya, da dama daga masharhanta na ganin ganawar ta yi armashi.

  • Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Zaben Gwamnan Zamfara A Matsayin Bai Kammala Ba
  • Sin Da Afirka Na Da Makoma Mai Kyau A Fannin Hadin Gwiwar Aikin Gona

Har ma wasu masu fashin baki na ganin shugabannin kasashen biyu, suna sane da cewa duniya ta zuba ido domin ganin rawar da za su taka a wannan gaba da duniya ke fuskantar manya manyan kalubale a mataki na kasa da kasa da ma na shiyyoyi.

Duniya ta yi imanin cewa, alakar Sin da Amurka tana da muhimmancin koli, kuma kyautatarta zai ingiza ci gaban duniya, don haka ya dace a yi duk mai yiwuwa wajen inganta ta.

Masu fashin baki sun dade da amincewa, cewa idan har Sin da Amurka suka juyawa juna baya, hakan zai haifar da mummunan sakamako ga duniya, baya ga illar da hakan zai yi a gare su, don haka ba hanya ce mai bullewa ba. Kaza lika ba abu ne mai yiwuwa daya daga cikin manyan kasashen biyu ta yi yunkurin sauya dayar ba, kuma rura wutar rikici, ko fito na fito tsakanin su ba zai haifarwa kowa da mai ido ba.

LABARAI MASU NASABA

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Tabbas, mummunar takara tsakanin manyan kasashe masu fada a ji ba ta dace da muradun wannan zamani ba, kuma hakan ba zai warware tarin kalubale da Sin da Amurka ke fuskanta, da ma matsalolin sauran sassan duniya ba. Don haka fatan dukkanin sassan kasa da kasa a wannan gaba da wadannan shugabanni na manyan kasashen duniya ke tattaunawa, shi ne su kai ga cimma nasarar dinke baraka, su rungumi juna, tare da amincewa cewa nasarorin da suke cimmawa, damammaki ne na bunkasar juna.

Ko shakka babu, muddin kasashen Sin da Amurka sun martaba juna, sun rungumi hadin gwiwar cimma moriya tare cikin lumana, bangarorin biyu za su cimma nasarar shawo kan sabanin dake tsakaninsu, tare da zakulo hanya madaidaiciya ta zaman jituwa mai alfanu. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya
Daga Birnin Sin

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103
Daga Birnin Sin

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Next Post
Akwai Kyakkyawan Fata Game Da Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka A Wannan Karo

Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Ba Da Tallafin Kudi Don Inganta Hadin Gwiwar Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”

LABARAI MASU NASABA

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

October 18, 2025
Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.