Wani jigon jam’iyyar APC a Jihar Kano, Ilyasu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, ya amince da hukuncin kotun daukaka kara tare da tarawa a zaben 2027.
Ya kuma gargadi Gwamna Yusuf kan tunkarar kotun koli bayan sha kaye a kotun sauraron kararrakin zabe da kuma kotun daukaka kara.
- An Kama Wadanda Ake Zargi Da Kai Wa Shugaban Kwadago Hari Ribadu
- Za Mu Kwato Wa Abba Hakkinsa A Kotun Koli – NNPP
Kwankwaso wanda tsohon Kwamishinan Raya Karkara ne a Jihar, ya yi wannan kira ne a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani kan hukuncin da kotun daukaka kara.
Ya kuma yaba da nasarar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna ya samu, inda ya bayyana tabbatar da zabensa a matsayin zababben gwamnan jihar a matsayin nasarar mulkin dimokradiyya.
Ya ce kamata ya yi Abba ya yi jiran tsimayin shekarar 2027 domin sake shiga zabe.
Ya yi nuni da cewa, yanzu da kotun daukaka kara ta soke nasarar da ya samu a zaben da ya gabata, yana da kyau ya zauna ya shirya sake tsayawa takara a shekarar 2027 a karkashin jam’iyyar siyasa.
Kwankwaso ya kara da cewa “A matsayina na dan uwa ina amfani da wannan kafar wajen ba shi shawarar da ya kawar da duk wani yunkuri na janyo masa rashin nasara a kotun koli, kawai ya yarda da hukuncin da aka yanke.”