Guda daga cikin fannin noma da ke bukatar a daga darajarsa a Nijeriya ta hanyar yin amfani da fasahar zamani shi ne, kula da shuka bishiyar kadanya, musamman ganin cewa nomansa na da matukar riba.
Bishiyar man kadanya, na daya daga cikin amfanin gona da ake samun kudaden shiga, wanda kuma yake taimaka wa wadanda suka rungumi fannin a fadin wannan kasa wajen rage musu talauci da halin kaka-na-ka-yi.
- Za Mu Kwato Wa Abba Hakkinsa A Kotun Koli – NNPP
- Gwamnonin Arewa Maso Yamma Na Yunkurin Zamanantar Da Aikin Gona
Sai dai kuma, masu ruwa da tsaki a wannan fanni na ganin cewa, babban kalubalen da fannin ke fuskanta shi ne, sama da kashi 98 cikin 100 na masu sarrafa shi a cikin gida, na yin amfani da dabarun gargajiya ne wajen sarrafa shi.
Wani masani a fannin aikin noma a kasar nan, Malam Yunusa Abdulhamid ya bayyana cewa, rashin nuna damuwa a kan shuka bishiyar man kadanyar; ya kara jawo wa fannin matukar koma baya a kasuwannin cikin gida da kuma ketare.
A cewarsa, wannan ya kawo wa kasuwancinsa koma baya matuka wajen samun riba da bunkasa. Ya zama wajibi a kara yawaitar shuka bishiyirasa ta hanyar yin amfani da fasahar zamani, in ji shi.
Haka zalika, ya kyautu gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen bunksa noman bishiyar man kadanya, domin samun gwaggwabar riba.
Bisa wani kundi da aka samu daga cibiyar bunkasa gudanar da binciken kayayyaki ta RMRDC, ana shuka bishiyar man kadanya ne a kimanin jihohi 21 daga cikin jihohi 36 da ake da su a fadin Nijeriya.
Bugu da kari, koko ko kwabsar da man kadanya ke zuwa a cikinsa, na dauke da kimanin ‘ya’ya 42 zuwa 48 wadanda ke gyara fatar jiki tare da yin amfani da shi wajen maganin gargajiya, sannan kamfanoni da dama na sarrafa shi zuwa wasu nau’ikan magunguna.
Har ila yau, ana amfani da man kadanya a girkin abinci tare da sarrafa alewa da sabulun wanka da man shafawa da sauran makamantansu.
Man kadanya na dauke da ma’aunin yanayi daga 32 zuwa 45, wanda hakan ya sa yake da saurin narkewa a lokacin da ake dora shi a kan wuta, domin sarrafa shi zuwa wani nauin da ake bukata.
Har wa yau, idan aka laakari da wasu rahotannin kasuwa da aka fitar a shekarar 2023 ya bayyana cewa, bisa kiyasi da aka yin a farashin man kadanyar a kasuwar duniya, ya kai kimanin dala biliyan 2.5 a shekarar 2021, inda kuma farashin ya kara tashi zuwa dala biliyan 2.8 a shekarar 2022.
Kazalika, ana sa ran farashin nasa zai iya karuwa zuwa dala biliyan 5.2 daga nan zuwa shekarar 2030, wanda aka kiyasata zai kai kashi 8 a cikin dari daga shekarar 2022 zuwa shekarar 2030.
Bugu da kari, Nijeriya ta kasance kan gaba wajen albarkatun bishiyoyin man kadanya a fadin duniya, wanda kuma take a kan gaba wajen samar da shi a fadin duniyar da ya kai kimanin kashi 45 cikin 100.
Har ila yau, kundin ya kuma nuna cewa, ana sarrafa man kadanya wanda ya kai daga tan 330,000 zuwa tan 350,000 a duk shekara.
Sai dai daga cikin tan 800,000 na man kadanyan da ake samarwa a kasar nan, tan miliyan 20,000 kacal ne aka iya amfani da shi a cikin gida sauran kuma ake fitar da shi zuwa kasashen da ke makabtaka ta Nijeriya.
Hakan ya faru ne, sakamakon rashin samar da shi a wadace, musamman domin cimma bukatar samar da ingancinsa da wadatuwarsa a kasuwar duniya.
Saannan, wadanda ke kokarin sarrafa shi a yankunan karkara, na yin amfani da dabarun gargajiya ne kadai wajen sarrafa shi.