ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Noman Kadanya: Yadda Rashin Amfani Da Fasahar Zamani Ke Dakile Samun Dimbin Riba

by Abubakar Abba
3 years ago
Kadanya

Guda daga cikin fannin noma da ke bukatar a daga darajarsa a Nijeriya ta hanyar yin amfani da fasahar zamani shi ne, kula da shuka bishiyar kadanya, musamman ganin cewa nomansa na da matukar riba. 

Bishiyar man kadanya, na daya daga cikin amfanin gona da ake samun kudaden shiga, wanda kuma yake taimaka wa wadanda suka rungumi fannin a fadin wannan kasa wajen rage musu talauci da halin kaka-na-ka-yi.

  • Za Mu Kwato Wa Abba Hakkinsa A Kotun Koli – NNPP
  • Gwamnonin Arewa Maso Yamma Na Yunkurin Zamanantar Da Aikin Gona

Sai dai kuma, masu ruwa da tsaki a wannan fanni na ganin cewa, babban kalubalen da fannin ke fuskanta shi ne, sama da kashi 98 cikin 100 na masu sarrafa shi a cikin gida, na yin amfani da dabarun gargajiya ne wajen sarrafa shi.

ADVERTISEMENT

Wani masani a fannin aikin noma a kasar nan, Malam Yunusa Abdulhamid ya bayyana cewa, rashin nuna damuwa a kan shuka bishiyar man kadanyar; ya kara jawo wa fannin matukar koma baya a kasuwannin cikin gida da kuma ketare.

A cewarsa, wannan ya kawo wa kasuwancinsa koma baya matuka wajen samun riba da bunkasa. Ya zama wajibi a kara yawaitar shuka bishiyirasa ta hanyar yin amfani da fasahar zamani, in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Haka zalika, ya kyautu gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen bunksa noman bishiyar man kadanya, domin samun gwaggwabar riba.

Bisa wani kundi da aka samu daga cibiyar bunkasa gudanar da binciken kayayyaki ta RMRDC, ana shuka bishiyar man kadanya ne a kimanin jihohi 21 daga cikin jihohi 36 da ake da su a fadin Nijeriya.

Bugu da kari, koko ko kwabsar da man kadanya ke zuwa a cikinsa, na dauke da kimanin ‘ya’ya 42 zuwa 48 wadanda ke gyara fatar jiki tare da yin amfani da shi wajen maganin gargajiya, sannan kamfanoni da dama na sarrafa shi zuwa wasu nau’ikan magunguna.

Har ila yau, ana amfani da man kadanya a girkin abinci tare da sarrafa alewa da sabulun wanka da man shafawa da sauran makamantansu.

Man kadanya na dauke da ma’aunin yanayi daga 32 zuwa 45, wanda hakan ya sa yake da saurin narkewa a lokacin da ake dora shi a kan wuta, domin sarrafa shi zuwa wani nauin da ake bukata.

Har wa yau, idan aka laakari da wasu rahotannin kasuwa da aka fitar a shekarar 2023 ya bayyana cewa, bisa kiyasi da aka yin a farashin man kadanyar a kasuwar duniya, ya kai kimanin dala biliyan 2.5 a shekarar 2021, inda kuma farashin ya kara tashi zuwa dala biliyan 2.8 a shekarar 2022.

Kazalika, ana sa ran farashin nasa zai iya karuwa zuwa dala biliyan 5.2 daga nan zuwa shekarar 2030, wanda aka kiyasata zai kai kashi 8 a cikin dari daga shekarar 2022 zuwa shekarar 2030.

Bugu da kari, Nijeriya ta kasance kan gaba wajen albarkatun bishiyoyin man kadanya a fadin duniya, wanda kuma take a kan gaba wajen samar da shi a fadin duniyar da ya kai kimanin kashi 45 cikin 100.

Har ila yau, kundin ya kuma nuna cewa, ana sarrafa man kadanya wanda ya kai daga tan 330,000 zuwa tan 350,000 a duk shekara.

Sai dai daga cikin tan 800,000 na man kadanyan da ake samarwa a kasar nan, tan  miliyan 20,000 kacal ne aka iya amfani da shi a cikin gida sauran kuma ake fitar da shi zuwa kasashen da ke makabtaka ta Nijeriya.

Hakan ya faru ne, sakamakon rashin samar da shi a wadace, musamman domin cimma bukatar samar da ingancinsa da wadatuwarsa a kasuwar duniya.

Saannan, wadanda ke kokarin sarrafa shi a yankunan karkara, na yin amfani da dabarun gargajiya ne kadai wajen sarrafa shi.

Kadanya
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    2027: An Shirya Wa Matasa Bita Kan Guje Wa Kalaman Kiyayya A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Za Ta Ƙirƙiro Da Tsarin Kamun Kifi A Tashoshin Jiragen Ruwa – Ɗantsoho
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    A Cikin Wata Shida Manyan Jiragen Ruwa 2,300 Suka Sauke Kaya A Tashoshin Jiragen Ruwa— Dantsoho
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Manyan Kalubalen Da Ke Durkusar Da Kiwon Kifi A Nijeriya

Manyan Kalubalen Da Ke Durkusar Da Kiwon Kifi A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA

October 24, 2026
Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

October 23, 2026
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

October 23, 2026
Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

October 23, 2026
Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026
Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

October 23, 2026
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.