Hukumar Hisba a Zamfara, karkashin jagorancin shugabanta, Sheikh Umar Hassan ya tabbatar da kama mata da maza masu badala dauke da Cutar Kanjamau a Gusau.
Sheikh Hassan ya tabbatar da haka ne yayin da wata kungiyar zawara masu hada Auren Sunna suka ziyarce shi a ofishinsa da ke Gusau.
- Ana Fatan Sakamakon Ganawar Xi Da Biden Zai Taka Rawa Wajen Kyautata Dangantakar Sin Da Amurka
- ‘Yan fashin Daji Sun Halaka Wasu ‘Yan Sa-kai 6 A Jihar Zamfara
Shugaban ya bayyana cewa, hukumar ta kama mata da mazan ne a lokacin da suka fita sintirin farautar masu aikata laifi a wuraren badala.
Acewarsa, “Hukumar Hisba ta gargadi maza da mata masu hulda da mutanen banza da suyi hattara da kansu, mun kama wasu masu badala mun kama gurfanar da su a gaban kotu bayan mun yi musu gwajin jini kuma sakamakon ya nuna da yawa suna dauke da cutar kanjamau.”
Da ya koma kan batun kungiyar zawara masu hada Auren Sunna, sheikh Umar Hassan ya yaba da ayyukan kungiyar ya kuma tabbatar da cewa, hukumar zata yi aiki da su kafada-da-kafada don ganin an samarwa zawarawan mafita mai kyau.
Anasu jawabin, Shugabanin Kungiyar zawarawan, Imamu Musa kura da Malam Sa’idu Koshe da Sani Takule, sun bayyana cewa, sun ziyarci hukumar ne don taya sabbin shugabannin hukumar murna da kuma neman hadakai kan cigaban kungiyar tare da hukumar Hisba don sauke nauyin da ke kan kungiyar na aurar da zawarawa a fadin jihar.
Kawo yanzun, kungiyar ta aurar da mata zawarawa fiye da 1,000 da kafuwar kungiyar.
kuma har yanzun, kungiyar na cigaba da aurar da duk bazawarar da ta samu miji, ana yi musu bikin take bayan kwamitocinmu sun kammala bincike akan ma’auratan.