A daidai lokacin da kotun daukaka kara ke ci gaba da zartar da hukunci game da shari’o’in zabe da aka daukaka daga kotunan sauraron kararrakin zabe, hukuncin ya haifar da cacar baki a tsakanin ‘yan adawa da gwamnati, wanda wasu suka fara zargin ana yi wa dimokuradiyyar Nijeriya kafar angulu.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa dimokuradiyyar Nijeriya na fuskantar barazana karkashin gwamnatin APC, wanda a yanzu a bangaren shari’ar Nijeriya na sayar da hukunci kudi-a-hannu.
- Zargin Baɗala: Hisba Ta Kama Mata Da Maza A Zamfara
- Zaben Kano: Abba Ya Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli
Atiku ya jaddada damuwarsa kan dorewar dimokuradiyyar Nijeriya da ke fuskantar barazana na yadda jam’iyya mai mulki ke amfani da kotuna waje tsege gwamnonin ‘yan jam’iyyar adawa a jihohin Nijeriya.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Paul Ibe ya fitar, ya ce ana raunata ‘yan adawa a Nijeriya ta hanyar yin magudin zabe da kuma amfani da kotuna ana amshe kujerunsu.
Ya kara da cewa, “Abin da ya fi daukar hankali shi ne, jihohin da kotuna suka yanke hukuncin cire gwamnonin dukkansu na jam’iyyun adawa ne. Tun daga Kano, Zamfara zuwa Filato, inda muke ganin cewa jam’iyya mai mulki ta kasa yin nasara a wadannan jihohi a lokacin zabe, amma kuma yanzu tana amsa a kotu.
“Wadannan alamu ne masu barazana ga harkokin zabe da bangaren shari’a tare da tabbatar da cewa dimokuradiyyarmu ta lalace. A bayyana yake jam’iyya mai mulki tana gudanar da mummunar akida ta kwace mulki daga hannun ‘yan adawa.
“Abin da ya fi daukar hankali shi ne, abin da ke faruwa a yanzu a game da zaben gwamnan Filato, wanda tun farko dan majalisar APC a wani faifan bidiyo ya yi barazanar cewa jam’iyya mai mulki za ta bi tsarin shari’a don tabbatar da nasararta a kotuna.
“Saboda haka, yana nufin cewa zamanin da muke ciki a zahiri abin tsoro ne, kuma akwai jan aiki a gabanmu wajen ceto dimokuradiyyarmu daga hannun wadannan masu neman mulki ko ta wani hali.”
Sai dai Atiku ya ce ya yi mamakin abin da ke faruwa a yanzu, inda ya ce a Jihar Legas inda Shugaba kas, Bola Tinubu ya fito ya zama ubangida, wanda an kashe ‘yan adawa, sannan an tilasta wa kowa ciki har da alkalai su shiga jam’iyyarsa.
- Obasanjo Ya Yi Tir Da Hukunce-hukuncen Zaben Gwamnoni
Tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya caccaki hukuncin da alkalan Nijeriya suka yanke kan shari’o’in zaben gwamnoni. Ya ce bai kamata alkalai uku zuwa biyar su soke hukuncin da miliyoyin masu kada kuri’a suka yanke a lokacin zabe ba.
Obasanjo ya bayyana ikon da wasu alkalai kalilan ke da shi a matsayin al’amari da ba za a amince da shi ba.
Tsohon shugaban kasar ya yi magana ne dangane da hukuncin da kotun daukaka kara ke ci gaba da yi kan takaddamar bayan zaden 2023 a Nijeriya.
A makon da ya gabata ne dai wasu alkalan kotun daukaka kara suka yanke hukuncin korar wasu gwamnoni uku daga kujerunsu.
Hukunce-hukuncen kotun daukaka karar sun janyo ka-ce-na-ce ne mai yiwuwa saboda duka gwamnonin jihohin da aka soke zabensu, na ‘yan adawa ne kamar babbar jam’iyyar adawa ta PDP da ke da Filato da Zamfara da kuma NNPP wadda ke da kujerar gwamnan Kano.
Lokacin da yake tsokaci a wani taron sake fasalin dimokuradiyya domin amfanin kasashen Afirka a birnin Abeokuta na Jihar Ogun, ya ce tsarin mulkin dimokuradiyya na kasashen Turawan yamma ba zai taba yin daidai da kasashen Afirka ba, kasancewar ba ya la’akari da ra’ayin mafi rinjayen al’umma.
- Ka Iya Bakinka, Kar Ka Zubar Da Kimar Shari’a – Gwamnati
Fadar shugaban kasa ta mayar da zazzafan martani kan kalaman tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, inda ya zargi alkalai kan hukuncin da suka yanke, da kuma zargin gwamnatin Shugaba Tinubu ke haddasa lamarin.
A wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar, ya gargadi tsohon mataimakin shugaban kasar kan zargin gwamnati mai ci tana markushe ‘yan adawa ta hanyar amfani da bangaren shari’a.
Ya ce ya kamata Atiku ya iya bakinsa, kar ya zubar da kimar bangaren shari’a da kuma alkalai kan cimma burinsa na siyasa.
Onanuga ya ce Shugaba Tinubu masoyin dimokuradiyya ne wanda bai tsoma baki cikin hukunce-hukuncen shari’a. Ya kara da cewa PDP ta yi nasara a shari’ar kotuna a jihohin Osun da Bauchi, inda aka tabbatar da nasarar gwamna Ademola Adeleke da Bala Mohammed.