Kamar yadda muke gani a zahiri, kasar Sin ta samarwa duniya gudummawar tsarin ci gaba cikin sauri tsakanin shekaru 10 da suka gabata, ta hanyar gabatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya” ko BRI. Cikin manyan nasarorin da wannan shawara ta samar akwai cike gibin zuba jari a fannin samar da manyan ababen more rayuwa tsakanin kasashe masu ci gaba da masu tasowa.
Kafin kaddamar da wannan shawara ta BRI, duniya musamman kasashe masu tasowa na da matukar burin samun masu zuba jari, to sai dai kuma cibiyoyin hada-hadar kudi da suka saba cudanya da su, ko dai ba za su iya ba, ko kuma ba su da niyyar yin hakan. Ana cikin wannan yanayi ne kuma, kasar Sin ta gabatar da shawarar BRI, wadda ta samu matukar karbuwa tsakanin kasashen duniya, musamman masu tasowa da masu rauni sosai.
- Xi Jinping Ya Gana Da Takwaransa Na Uruguay
- Messi Da Ronado Za Su Hadu A Wani Wasan Sada Zumunci A Watan Fabrairu
Sai dai wani abun lura a nan shi ne yadda wannan shawara mai matukar tasiri ga samar da ci gaba, ke ta shan suka tun kafuwarta kawo yanzu. Tabbas abun takaici ne ganin yadda wasu ’yan siyasar yammacin duniya suka dage sai sun shafawa shawarar BRI kashin kaji ta hanyar kitsa karairai, da sharri iri-iri. Har ma wasu na kiran ta da “tarkon bashi”, ko “shirin tsoma hannu cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe”, ko ma “sabon salon mulkin mallaka” da dai sauransu.
Har ila yau, cikin irin wadannan ’yan siyasa da masu goya musu baya cikin jagororin wasu sassa, akwai masu amfani da kalmar dimokaradiyya a matsayin makami. Inda har kullum suke sukar tsarin dimokaradiyyar kasar Sin, da salon jagorancin al’ummarta, duk da cewa abu ne a zahiri, salon mulkin kasar Sin ya yi nasarar ciyar da kasar gaba, ya kuma ba da damar tsame miliyoyin al’ummar Sinawa daga kangin talauci, har ma kasar ta kai ga shiga sahun kasashe masu daidaitaccen tsarin tattalin arziki, kuma wuri da masu zuba jari ke rububin shiga.
Ko shakka babu, la’akari da wadannan dalilai, za mu gane cewa, sama da ko wane lokaci a tarihi, a yanzu duniya ta fi bukatar kadarori irin shawarar BRI, domin tabbatar da kyautatuwar rayuwar bil Adama, sabanin duk wata farfaganda maras tushe, wadda ba za ta amfani kowa ba, sai ma dai ruwa wutar rashin jituwa, da nunawa juna yatsa, da haifar da fito-na-fito.
Karin karbuwa da shawarar BRI ke samu tsakanin sassan kasa da kasa, ya nuna yadda al’ummun duniya ke kara maraba da sabon salo, kuma sabuwar turbar ci gaba, da ma kyakkyawar alkiblar da duniya ke fuskanta.
Duniya ta rungumi ci gaba tare, da warware matsalolin bil Adama cikin hadin gwiwa, maimakon kara bullo da wasu sabbin matsaloli. Don haka shawara ga sassan ’yan siyasar yammacin duniya, ita ce su rungumi hadin gwiwa da dukkanin sassa, domin cimma fa’ida ga kowa. (Saminu Alhassan)