A yau Alhamis aka bude taron baje kolin hakkin mallakar fasaha karo na 9 a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin, inda aka bude wani dandalin tattaunawa a gefe taron baje kolin.
Baje kolin na yini 3 ya hada da masu baje hajoji ta kafar intanet da na zahiri dake nuna sabbin nasarorin da aka samu da kayayyaki da fasahohi a masana’antar mallakar fasaha ta Sin. Dandalin tattaunawar kuma, zai karbi bakuncin wasu kananan dandali biyu da suka hada da na hadin gwiwar Sin da Afrika kan hakkin mallakar fasaha da rawar da hakkin mallaka ke takawa a bangaren gadon al’adu.
- Me Ya Sa Shirin Kasar Sin Dangane Da Batun Palasdinu Da Isra’ila Ya Samu Amincewar Duniya?
- Xi Ya Yi Alkawarin Hada Hannu Da Milei Domin Kyautata Huldar Sin Da Argentina
Tun bayan da aka kaddamar da shi a shekarar 2008, taron baje kolin ya kasance wani muhimmin dandali na nuna ci gaban kasar Sin a bangaren kare hakkin mallakar fasaha da inganta musaya a masana’antar mallakar fasaha ta duniya da saukaka cinikayya a masana’antar
A yau Alhamis, hukumar kula da hakkin mallakar fasaha ta duniya WIPO da hukumar kula da hakkin mallakar fasaha ta kasar Sin suka gabatar da lambobin yabo da suka hada da lambar yabo ta fasahar kirkire-kirkire da na amfani da fasaha da na kariyar fasaha da na tafiyar da harkokin mallakar fasaha. (Fa’iza Mustapha)