Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika wasikar taya murna ga baje kolin cinikayyar digital na kasa da kasa karo na biyu a yau Alhamis.
A cikin wasikar tasa, Xi ya bayyana cewa, a halin yanzu, cinikayyar digital tana bunkasa sosai, kuma ta zama abin dake jan hankalin mutane kwarai ta fuskar cinikayyar kasa da kasa.
- Gaza: Isra’ila Ta Kashe Mutum 14,200, Daga Ciki Yara 6,000, Mata 4,000 – Jakadan Falasdin
- Li Qiang Ya Halarci Taron Shugabannin G20 Da Aka Gudanar Ta Kafar Bidiyo
Ya ce a cikin shekarun baya bayan nan, Sin tana aiki tukuru wajen daidaita ka’idojin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa bisa babban matsayi, ta gina da kuma gyara tsarin jagorancin cinikayyar digital, ta inganta ci gaba da kirkire-kirkiren kwaskwarimar cinikayyar digital, ta dade da samar da sabbin damammaki ga duniya ta hanyar sabon ci gaban Sin.
Kaza lika kasar Sin na fatan bangarori daban daban za su yi amfani da dandalin baje kolin cinikayyar digital na kasa da kasa, su tattauna hadin gwiwa tare, su inganta ci gaba tare, kuma su raba sakamakon ci gaba tare, kana su mayar da cinikayyar digital zuwa wani sabon injin dake tafiyar da ci gaba tare, ta yadda za a zuba sabon karfi ga karuwar tattalin arzikin kasa da kasa.
An bude baje kolin cinikayyar digital na kasa da kasa karo na biyu, a yau din a birnin Hangzhou, bisa jigon “Cinikayyar digital ta hade duniya baki daya”. (Safiyah Ma)