Cikin wasu Satika da suka gabata a wannan dandamali, an yi wani tsokaci game da sha’anin ruguzau da Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke yi a Kano, mai taken “Ruguzau A Kano : Ra’ayin Masu Zabe Ne”. Dukkan lamari a ilmance, ana kallonsa ne ta mahanga iri daban daban, wanda haka manyan Shehunan Malamai na addini da na zamani suka nusar a fagen ilimi.
A wancan tsokaci namu, an kalli lamarin ruguzau din ne ta mahangar kamfen da gwamnatin Abban ta yi tun azal, cewa, idan ta sami sukunin darewa bisa kujerar gwamnan Kano, za ta rugurguje duka tarin dukiyoyin da al’umar jihar Kano suka mallaka ba bisa ka’ida ba daga hannun gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje! Bayan samun nasarar Abban, sai kuwa ta rika bi sako da lungu tana ragargaje wadancan kadarori na biliyoyin kudade.
- Shugaban Africa CDC Ya Yaba Da Hadin Gwiwar Sin Da Afrika A Bangaren Kiwon Lafiyar Al’umma
- Masana Sun Yi Gargadi Kan Amfani Da Wani Sinadarin Gishiri A Nijeriya
Kallon irin wancan mummunar ruguzau da ba a taba gani ba a Kano, ta wata mahanga ko alkibla daban, sabanin alkawarin kamfen, ba laifi ne ba. Kawai dai, duk wata mahanga da za a kalla ko fassara wani al’amari, babban abin la’akari shi ne HUJJA!!!. Ita kanta kalmar SIYASA, mashahuran masana, sun kalle ta ne ta fuska ko mahanga iri daban daban; da Aristotle da Easton da Laski da Dahl da sauransu, ba ta mahanga iri guda ne ba, suka kalli tare da fassara Kalmar Siyasar ba (Baker, 1962 : 1; Dahl, 1950, 1- 5; Easton, 1957: 383-400; Laski, 1930; Fagge & Alabi, 2007: 87-88).
A takaice, kallon ruguzau a Kano, ta fuskar mummunan kazgaro da miki da al’umar Kano ta yi gamo da shi ta fuskar tattalin arzikinsu, ba zai zama wani abin aibu ba. Wasu na fassara sha’anin na ruguzau da cewa, an kaucewa ka’idar duka Shari’ar Addini da ma ta Zamani wajen aiwatar da shi. Wasu ko, na fassara mummunar tirjiya da rudu da rashin sanin makoma, da gwamnatin Abba Kabir Yusuf din ke haduwa da shi, a Kotunan Shari’ar Zabe a yau, ba wani abu ne ba, face alhakin dubban mutanen da gwamnatin ta kassara ne a Kano, da sunan huce haushin Kwankwaso a kan Ganduje. Alhali, hatta a addinance, laifin wani ba ya shafar wani. Hatta ma a ita kanta shari’ar Baturen.
Wannan tsokaci namu na yau, zai bibiyi lamarin na wancan rusau ne, ta mahangar an yi sanadiyyar karairayewar arzikin jama’ar Jihar Kano, manyansu da yaransu, tare da bibiyar, shin, an aiwatar da rusau din kuwa bisa tanadin Doka da Oda. Babu shakka, idan ya zamana bincikenmu ya tabbatar cewa, ba a bi turbar doka sau da kafa wajen yin ruguzau din ba, sannan, an karya tattalin arzikin mutane, cikinsu har da dubban MARAYU, to fa batun ALHAKI KWIKWIYO na iya samun gindin zama a gidan gwamnatin jihar Kanon.
…Sai Mun Dawo Da Wuraren Da Aka Sacewa Gwamnati…
Maganar sai an dawo da wuraren da gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta mallakawa wasu mutane a Kano, ta zamo guda daga manyan ababen da Abba Gida Gida da uban gidansa Kwankwaso suka rika fadi a matsayin kamfen din babban zaben Shekarar 2023 da ke kara fuskantowa. Saboda haka, bayan rantsar da Abban da wasu awanni a Kano, sai maganar kwace wadancan kadarori na gwamnati ta zama danya, sabuwa ful, ba tare da wani bata lokaci ba, sai gwamna Abba ya fara shirye shiryen aiwatar da waccan manufa ta gwamnatinsu, da suka sanar da jama’a a lokacin yakin neman zabe.
Shin, wai gwamnatin Abba Gida Gida ba ta da hurumin kwato wasu kadarori na gwamnati daga wajen wasu jama’a a Kano? Amsar wannan tambaya, ita ce amsar shin wai, Dr Umar Ganduje bai da hurumin mallakawa wasu mutane a Kano filaye? Duka amsar guda ce, na’am, suna da cikakken iko da hurumi, sai dai abu na gaba da ya wajaba a kansu shi ne, wajen zartar da wancan iko nasu, wajibinsu ne su kula tare da dabbaka tanade-tanaden doka da oda. Ma’ana, yaya doka ta sahale musu BAYARWA da AMSHEWA?, sabanin haka, suna iya zama AZZALUMAI, ko da kuwa kullum a Haramin Makka ne suke Sallar Isha’i, sai dai a yaudari jahilai amma haka batun yake.
Ruguzau Da Rusau A Kano
Ba tare da wani bata lokaci ba, kwanaki biyar (5) da rantsar da Abba Kabir Yusuf (AKY), ya fara jan ayarin jama’a zuwa ga rushe dukiyar wasu al’umar Kano, da sunan cika alkawarin da suke yawan jan-kunnen jama’ar Kano, cewa, su daina yin gine-gine a wuraren gwamnati, ko da kuwa gwamna da doka ne suka sahale musu. A baya, mun nusar da gwamna Abba na da hurumin kwace wurare a Kano, tabbas haka ne, sai dai ta yaya ne zai yi kwacen? Zai kwace ne ta yadda Madugun Jar Tagiya Kwankwaso ya tsara masa ne, ko kuwa zai aiwatar ne bisa yadda Doka ta tsara? Babu shakka, nan ne zuzzurfan ramin da Abba Kabir ya rufta, shi ne kuma silar mummunan yanayi da fargabar da Kwankwasawan Kano suka tsinci kansu ciki a Siyasar Kano a yau. Wannan ba wai hasashe ne ba da ke fitowa daga bakin magautansu a siyasa ba, da yawan Kwankwasawan ne ke fadin haka, yayinda suka ja gefe a tsakaninsu.
Kwanaki biyar (5) da shigar Abba ofis a matsayin Gwamnan Kano mai cikakken iko ne, sai aka wayigari ya fito da manya manyan motocin ruguzau, karkashin jagorancin dandazon jami’an tsaro, suka nufi gine-ginen Filin Sukuwa (Race Course) na Kano, tare da ragargaje su!. Akwai katafaren gini hawa uku, kunshe da shaguna casa’in (90), amma duka maigirma gwamna ya sa aka rushe su nan take. A daya hannun kuwa, cincirindon matasa ne sanye da jajayen huluna, suna shewa tare da daka-wawa ga daukacin duk wani abu mai amfani da ke cikin wadannan shaguna da aka rushe, tare da wawashe duk wata kofa, ko taga, ko rodi da makamantansu, da sunan GANIMA.
Hanyoyin Kwato Kadarorin Gwamnati
Babu shakka, wannan rusau da Abba Gida Gida ya jefa kansa ciki, kasa da rantsar da shi da Sati guda, shi ne wani babban munkari abin-ki da ya fara aiwatarwa karkashin mulkinsa, kuma shi ne wani babban al’amari da ya tasamma rusa shi da kuma siyasarsa tun daga wancan lokaci. Wasu masana doka suna masu karin hasken cewa, a duk sa’adda gwamnati ke son yin dawaiya da wasu kadarorinta, ga hanyoyin doka da ya kamata a ce ta bi; 1- Farko, gwamna zai kafa wani Kwamiti ne, aikin wannan Kwamiti ne ya binciki yadda mutum ya mallaki wannan fili daga gwamnati. Bugu da kari kuma shi ne, ta yaya ne ma kuma mutum ya sami sahalewar gina wannan waje a gwamnatance?
2- Bayan wancan kwamiti da gwamna ya nada ya kammala bincikensa, sai ya tattara sakamakon binciken ya kai wa Kwamishina. 3- Shi kuma kwamishina, zai dauki wannan rahoto ne ya ta fi da shi zuwa zaman tattaunawa da hukumar zartaswa ke yi da gwamna a duk mako (za a ga cewa mafi yawan mambobin hukumar ta zartaswa kwamishinoni ne) don a hadu a tattauna. Bayan an tattauna, kuma gwamna ya zartar da rusau din, ko waninsa. 4- Sai a sake dawowa da kwamishina da wannan rahoto. 5- Sai shi kuma kwamishina zai aike da rahoton ne zuwa ga ofishin babban Sakatare (Pharm. Sec.). 6- Shi kuma babban sakatare zai tura wannan rahoto ne zuwa ga ofishin wani daraktan da abin ya shafa. 8- Da haka da haka umarni da ka’idojin aiki za su yi ta gudana har a je zuwa ga mataki na karshe da direba zai dauki murgujejiyar motar da za a je a yi rusau ko ruguzau din.
Idan mai karatu ya bibiyi waccan hanyar ta Sama ta bin doka da aka wassafa, wadda gwamnatin Abba Yusuf ya wajaba ta bi, yayin kwace wuraren da Ganduje ya mallakawa wasu jama’ar Kano, za a ga cewa kwata-kwata ma, ba tare da kafa wancan kwamitin ba, babu wata kofa halastacciya da Abban zai yi togo da ita, na halascin wancan ruguzau da ya yi. Sannan, ba tare da ya nada kwamishinoni ba, ta yaya ne za a aiwatar da ruguzau din bisa doron doka? Duk da kiraye kirayen da masana suka rika faman yi wa Abban, na ya dakanta ya fuskanci turbar doka wajen ragargaje dukiyoyin jama’ar Kano, sai hakan ya ci tura, tun da gwamnan ya ci gaba ne abinsa. Ba a kafa wancan kwamiti ba da doka ta nema, haka su ma kwamishinoni ba a nada su ba, tun da kwanakin gwamnatin biyar ne kacal ta fara rushe-rushen.
Har ila yau, Abba Kabir Yusuf, ya zabura zuwa wasu wurare da aka kashe musu biliyoyin kudade tare da ragargaje su, wurare irinsu Daula Hotel, da Haji Camp da Gine Ginen Filin Idi da sauransu, inda ta ragargaje dukiyar da ta kere naira miliyan dubu dari biyu da ashirin da shida (N226b). Wani abin tausayi ga akasarin masu irin wadannan wurare shi ne, sun bi halastacciyar hanya ne na mallakar wuraren daga gwamnatin da ta gabata, amma a banza! An bi ta haramtacciyar hanya an raba su da wurin, da sunan sun kauce ka’ida. Shin wai mai karatu, tsakanin wadanda suka mallaki irin wadancan wurare da kuma gwamnatin Abba, waye ya saude halastacciyar hanyar doka? Wani abu da zai girgiza duk mai imani shi ne, a kullum Abba Kabir Yusuf ya bude baki, za a ji yana cewa, kwata-kwata ba ya yin nadamar ruguje irin wadancan wurare da ya yi. Ashe yanayin shari’ar zaben Kano ba shi da nasaba da abin da aka yi wa irin wadannan mutane?
Da yawan mutane sun rasa rayukansu a sanadiyyar irin wannan ruguzau din da gwamnatin NNPP ta yi a Kano. Wani al’amari da ake fassara shi da keta shi ne, da daman wurare, ba a sanar da masu wurin hakikanin lokacin da za a je a yi musu rusau din. Sai dai kawai mutum ya je kasuwa ya tarar, da kayan shagon, da kudin da ke ciki, da ma kofofi da tagogi da rodinan ginin nasa duka an kwashe da sunan ganima! Ko mai karatu ya san adadin mutanen da suke yanke jiki suna faduwa a Kano, a lokacin wancan ruguzau din? Daga faduwar, wasu su mutu nan take, wasu sashin jikinsu ne ke shanyewa. Da daman marayu sun gwammace su bi iyayensu zuwa Lahira su huta. Dukiyar da aka tattare kudin gado aka mallaki waje, ko dai a na karbar kudin haya, koko a na gudanar da harkar kasuwanci, sai ake wayar gari, Abba Yusuf na ruguza su ba kakkautawa.
Alkalai Sun Fi Abba Adalci
Da yawan mutane a Kano a yau, na da tunanin cewa, irin wadannan Alkalan Kotunan Zaben da Kwankwasawan Kano ke antayawa zagi dare da rana, alamu na nuna sun ma fi gwamnatin ta NNPPn Kano adalci. Hujjarsu ita ce, a duk sa’adda wadancan alkalai suka zartar da wani motsi ko wani hukunci, sai an sami wata sadara daga sadarorin Kundin Tsarin Mulki Na Kasa ko Kundin Dokar Zabe da suka dogara da shi. Da wace sadara Abba ya dogara da ita, na yin rusau a Kano? Ashe mai karatu bai san wata Kotu ta nemi Abban da ya biya irin wadancan mutane biliyoyin kudade ba a Kano? Wani abin takaici, a kullum burin Abba shi ne a gama shari’ar zabe, ya koma ya ci gaba da irin wancan ruguzau, tun da haka Madugu ke so a yi, anya kuwa yana neman nasara a Kotun?
Wani lamari na rashin adalci karara shi ne, tun gabanin Ganduje ya fara bayar da filaye a gefen makarantu a Kano, Kwankwaso ne ya fara yi. Mutum ya je unguwar Kabuga jikin katangar Jami’ar Bayero, Kano, zai ga wuraren da Madugun Jar Hular ya ba da. Da wani zai musa, sai a zo da wurare sama da hamsin (50), wadanda Kwankwason ya ba da, amma gwamnatin Abba ta haramtawa wadanda Ganduje ya bai wa irinsu a garin na Kano. Bugu da kari, yayinda gwamnatin Abban ta taho titin BUK Road a Kano, tana gogawa gine-ginen da za ta rushe jan-fenti, a duk sa’adda ta zo wani wuri da Kwankwaso ya bayar, sai ta tsallake, a tafi wajen da Ganduje ya bayar, nan ma idan akwai mai musantawa, sai a gabatar masa da HUJJOJI. Wani abin rufa-rufar, sai misalin karfe 2am na dare ko karfe 3am na dare ne ake fita wajen yin ruguzau din, tare da gungun matasa masu halasta haramun da sunan GANIMA!
Wani abin takaici shi ne, lokacin da ake tsaka da irin wancan ruguzau wai kuma sai a ji mai magana da yawun gwamna, Sunusi Bature D/Tofa na cewa, da jama’ar Kano, su yi hakuri, gwamnatin Abba na nan tana aiki tukuru, don ganin arzikin garin Kano ya yawaita nan gaba. Ashe kwai a baka, bai fi kaza a akurki ba? Ashe arzikin mutanen da gwamnan ke ragargajewa, bai fi zama tabbas a gare su ba? Idan a na yaudarar za a sami arziki nan gaba daga gwamnati, to yaya za a yi da wadanda suka rasa rayukansu a dalilin rusau din? Yaya kuma wadanda jikinsu ya shanye da makamantansu, wadanda aka wayigari lafiyar ma suke nema kafin a kai ga wani dadin baki da za a yi musu na dukiya?