Ministan Albarkatun Ruwa, Farfesa Joseph Terlumun Utseb, ya kaddamar da shirin noman rani; wanda aka yi wa lakabi da ‘Rafin-Yashi’.
Haka zalika, shirin ya kunshi samar da kadadar noma sama da guda 28 da kuma gonar Songhai da ke karkashin hukumar kula da kogin Neja, domin kara habaka noman rani tare da lalubo mafita a kan karancin abinci a fadin wannan kasa baki-daya.
- NPA Ta Gargadi Masu Jibge Kwantaina Ba Bisa Ka’ida Ba
- Gwamnatin Kano Ta Dawo Da Ma’aikatan Da Ta Dakatar Da Ganduje Ya Ɗauka Aiki
Sannan Minsitan, ya kaddamar da tankunan ruwa sama da 700,000, wadanda za a iya adanawa tare da yin tanadin ruwa domin yin noman rani.
A cewar tasa, “daya daga cikin tankunan ruwan; za su rika yin amfani da shi wajen tura ruwa zuwa Rafin-Yashi, domin aiwatar da noman rani, inda sauran kuma za a rika amfani da su wajen tura ruwa zuwa gonar Songhai.
Har ila yau, Dam din Rafin Yashi, wanda guda ne cikin ayyukan da ministan ya kaddamar, ya kai zurfin kimanin kafa 650,000, wanda ko shakka babu zai yi matukar taimakawa; wajen rage ambaliyar ruwan sama a tsakanin al’ummar da ke zaune kusa da Dam din na Rafin Yashi,” in ji shi.
Ministan ya kara da cewa, idan aka kammala aikin wannan Dam, zai taimaka wajen samar da wutar lantarki da noman rani tare da taimakawa wajen kirkiro da ayyuakan yi da farfado da tattalin arzikin wannan kasa da kuma habaka samar da wadataccen abin abinci, wanda hakan ya yi daidai da kudire-kudiren Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.
Bugu da kari, ya sanar da cewa, a makon da ya gabata; ma’aikatarsa ta kaddamar da ayyukan noman rani na shekarar 2023, domin bunkasa samar da wadataccen abinci a fadin kasar.
Ministan ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Neja, ta samar da wadatacciyar kasa a Hukumar Kula da Kogin Neja, domin a rika yin noman rani, don amfanin jihar da kuma kasa baki-daya
Kazalika, ya sanar da cewa; akwai bukatar Gwamnatin Jihar ta samar da kayan aikin noman rani tare da bai wa ‘yan jihar kwarin guiwar rungumar yin ayyukan na noman rani, a cewar tasa wannan hanyar ce kadai za a kara samar da wadataccen abinci a fadin dukkanin wannan kasa.
Har wa yau ya kara da cewa, dole ne a samar da wadataccen abinci ga kafatanin ‘yan Nijeriya da kuma wanda za a rika fitarwa zuwa kasashen ketare.