Kimanin alhazai miliyan daya da suka hada da jimillar mutane 42,000 daga Nijeriya, sun hallara a Dutsen Arafat domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2022 a ranar Juma’a.
Alhazan za su shafe tsawon yini guda a Dutsen Arafat a matsayin daya daga cikin manyan wuraren ibadar Hajji kafin su wuce zuwa Muzdalifah, inda za su kwana, sannan su koma Muna a ci gaba da gudanar da aikin hajji.
- Al’ajabi: Yadda Wani Maniyyaci Ya Fara Aikin Hajjinsa A Sansanin Alhazai Na Kano Bayan Rasa Kujerarsa
- Wani Dan Afrika Ta Kudu Ya Isa Birnin Makka Don Yin Aikin Hajji Bayan Shafe Tafiyar Shekaru 3
Tsayuwa a Arafa wani muhimmin bangare ne na aikin Hajji domin wuri ne da Allah yake karbar dukkan addu’o’in da mahajjata ke yi.
Ana sa ran mahajjata za su yi amfani da ranar don yin addu’o’i ga kansu, iyalai, abokai, al’uma, kasashe da duniya baki daya.
Dutsen Arafat kuma ana kiransa da Jabal ar-Rahmah, ma’ana dutsen rahama.
A rana ta tara, mahajjata suna tashi daga Muna zuwa Dutsen Arafat inda suke tsaye cikin tawassuli da addu’o’i da karatun kur’ani.
A Dutsen Arafa ne Annabi Muhammad (S.A.W) ya yi hudubarsa ta karshe ga Musulmi wadanda suka raka shi aikin Hajji a karshen rayuwarsa.
Aikin Hajjin Mahajjaci ana ganin ba shi da inganci idan ba su yini ba a Dutsen Arafat.
A halin da ake ciki, Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta nemi afuwar daukacin alhazan Nijeriya na rashin samun Samar zuwa aikin hajjin 2022 da wahalhalu da rashin jin dadi da suka fuskanta a yayin da ake jigilar jiragen sama zuwa kasa mai tsarki a kasar Saudiyya.
Hukumar ta kuma nemi irin wannan afuwar ga gwamnatin tarayyar Nijeriya, da hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi da kamfanoni masu gudanar da jigilar Alhazai masu zaman kansu, da sauran jama’a kan duk wani abin rashin jin dadi da lamarin da ya faru a ‘yan makonnin da suka gabata ya jawo.
Hukumar ta bayar da hakuri na musamman ga maniyyata 1,552 da suka fito daga jihohin Bauchi, Filato da Kano da kuma wadanda ke karkashin masu gudanar da jigilar maniyyata ta Jiragen yawo da ba su samu damar zuwa wannan aikin Hajjin ba saboda koma bayan da aka samu a cikin mintunan karshe da ya kawo cikas ga shirinta na kammala jigilar alhazai kafin rufe filin jirgin sama na Jeddah. .
Alhazan da abin ya shafa sun hada da: maniyyata tara daga jihar Bauchi; Mahajjata 91 daga jihar Filato; Mahajjata 700 daga jihar Kano da kuma mahajjata kimanin 750 daga bangaren masu Jigila ta Jiragen yawo masu zaman kansu.
Hukumar a cikin wata sanarwa da ta fito daga mataimakiyar daraktarta kan harkokin jama’a, Hajiya Fatima Sanda Usara, ta tabbatar wa daukacin alhazan da abin ya shafa cewa za a mayar musu da kudin aikin Hajjinsu yayin da NAHCON za ta yi kokarin inganta nakasunta a shekarar 2023.