Shirye-shiryen Kungiyar ‘Incentives For All Child’ ya samu gagarumar nasarar a jihohi tara na yankin Arewacin kasar nan, shugaban shirin wanda kuma babban sakataren ne a ma’aikatar lafiyar Jihar Gombe, Alhaji Muhammad Ibrahim Jalo ne, ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki na Jihohin Adamawa, Bauchi, Gombe, Taraba, Kaduna, Jigawa, Kano, Katsina, Sokoto, Zamfara da Jihar Kebbi.
Sakamakon kyakkyawan shirin wannan kungiyar ta ‘Incentives for All Child’, yanzu haka Jihar Gombe ta samu kyakkyawan yabo bisa yadda ta aiwatar da kyawawan manufofin wannan shiri, don haka sai ya bukaci jihohin su ci gaba da bada himma domin ganin jarirai na kara samun kulawar da ta kamata, wanda zuwa yanzu a wannan shekara ‘New incentives’ ta samu nasarar yi wa jarirai sama da miliyon biyu rigakafi, wannan ko shakka babu jami’an shirin da su kara hazaka don sauke wannan nauyi.
- Barcelona Ta Tsallaka Mataki Na Falan Daya Bayan Doke Porto
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Fito Da Manhajar DSO Na Aikin Talbijin Kwanan Nan – Minista
Shi ma a nasa jawabin ga manema labarai, mataimakin jami’in tsare-tsaren shirin na ‘New Incentive’, Muhammad Mubarak Bawa, ya bayyana irin nasarar da aka samu wadda ya ce duk shekara suke gudanar da irin haduwa, inda ake tatatuna nasarori da kuma matsalolin da aka fuskanta domin samar da nagaratacciyar mafita zuwa yanzu shirin ya samu gagarumar nasara a jihohi tara da ake gudanar da irin wannan sabon shiri wanda zuwa yanzu babu shakka kwalliya ta biya kudin sabulu, sannan ya jadadda aniyar shirin na ganin an kara samun karbuwarsa, musamman ganin a baya idan aka ce ga masu allurar rigakafi shi kenan sai fara boye yara da jarirai.
Jami’in shirin a Kano Alhaji Mukhatar Rabi’u Abubakar, ya bayyana cewa babu shakka zuwan wannan shiri na ‘New Incentives for All’ ya taimaka kwarai da gaske, musamman ta yadda muke kara himmar lura da ayyukanmu, kasancewar wannan hukuma na da tsarin kulawa da bibiyar yadda ake tafiyar da wannan shiri a dukkan jihohin da ake gudanar da shiri, ya ce akwai matakai daban-daban da wannan shiri ya shafa kama daga bangaren mahukunta, iyaye da kuma masu ruwa da tsaki, zuwa yanzu wannan shiri ya samu gagarumar nasara, ta yadda a baya za ka tarar da jami’in aikin allurar rigakafi da kyar a wuni ake iya yi wa yara biyar zuwa goma, amma yanzu kullum ana iya samun sama da yara 100 a kowace cibiya, saboda haka wannan abin a yaba wa wannan shiri ne kwarai da gaske.
An gudanar da taron masu ruwa da tsakiin na shirin ‘New incentives for Child’ na jihohin tara a ranar Talata a Otal din Tahir da ke Kano.