Kungiyar kwallon kafa ta Fc Barcelona ta samu tikitin buga zagaye na gaba a gasar Uefa Champions League bayan doke Fc Porto.
Ranar Talata ne Barcelona ta buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta Fc Porto kuma ta doke ta da ci 2-1, wanda hakan ya sa ta samu nasarar tsallake matakin rukuni-rukuni na gasar.
- Yau Tinubu Zai Gabatar Kasafin Kudin 2024
- An Gudanar Da Dandalin Sada Zumunta Na Basi Na Shekarar 2023
Pepe ne ya fara jefa kwallo a ragar Barcelona kafin tagwayen kasar Portugal Joao Cancelo da Joao Felix su sanyaya zuciyar Koci Xavi da magoya bayan Barcelona da kwallaye biyu da suka zura a mabanbantan lokuta.
Talla