Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudurin kasafin kudinsa na farko ga majalisar dokokin Nijeriya.
Kasafin kudin na shekarar 2024, wanda ya kunshi sama da Naira tirliyan 27.5 zai mayar da hankali wajen karfafa tsaron kasa da samar da aikin yi da harkokin zuba jari da rage fatara a tsakanin al’umma.
- Za Mu Gudanar Da Bincike Kan Kundin Takardun Shari’ar Zaben Gwamnan Kano – NJC
- Zaben 2023: NNPP Ta Ci Zabe Ta Hanyar Magudi A Kano – Doguwa
Shugaba Bola Tinubu ya ce an tsara kasafin kudin na shekara mai zuwa ne bisa hasashen sayar da gangar man fetur daya a kan dala 77.96, da hako kiyasin ganga miliyan 1.78 ta man fetur a kullum.
Kazalika za ake canjar da dalar Amurka daya a kan canjin Naira 750.
Kasafin kudin ya yi kudurin kashe Naira tirliyan 9.92 a bangaren ayyukan yau da kullum.
Sai kuma Naira tirliyan 8.25 wajen biyan bashi, yayin da manyan ayyuka za su samu Naira tirliyan 8.7.