Xu Ercai da matarsa Lu Ying, mutanen gundumar Minqin ne dake arewa maso yammacin kasar Sin, gundumar da ke iyaka da Hamadar Tengger da Badain Jaran suke ta bangaren gabas, da yamma da arewa.
A baya kaso 94.5% na yankin ya kasance Hamada. Adadin ruwa dake konewa ya haura yayyafin dake sauka da sama da ninki 20. Mazauna wurin na fama da matukar talauci saboda matukar karancin ruwa.
- Sin Na Ba Da Gudummawa Wajen Samar Da Abinci Da Tsarin Samar Da Kaya A Duniya
- An Kammala Aikin Bututun Karkashin Ruwa Na Sabuwar Hanyar Sin Da Ta Ratsa Teku
A shekarar 2017, a karon farko gwamnatin kasar Sin ta gabatar da tsarin farfado da kauyuka. Xu Ercai da matarsa sun fara gwada shuka kayan lambu bisa kyawawan manufofin da aka samar.
Ruwa na da muhimmanci matuka ga aikin shuka kayan lambu. Manufofin na taimakawa manoma wajen kafa bututu, don janyo ruwa daga madatsar ruwa zuwa wajen ban ruwa.
Ya zuwa yanzu, Xu Ercai da matarsa na kula da gona mai fadin kadada 733 karkashin tawagar hadin kai, inda suke shuka kayan lambu har nau’o’i 12.
Nagartattun manufofi da kimiyyar zamani sun fidda wata sabuwar hanyar kawar da talauci ga manoma a Minqin, wadda ta zama karfin inganta bunkasuwar kauyuka. Ci gaban da ake samu, ba ma kawai kimiyya ta taka rawarta ba ne, har ma ya zama misalin yadda ci gaban da aka samu wajen zamanintar da kasar Sin ke haifar da alfanu ga al’umma, kuma ainihin mataki ne da gwamnatin ke dauka na tabbatar da tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, kuma sabon salo na wayewar kan Bil Adama. (Mai zana da rubuta: MINA)