Shugabannin jam’iyyar APC a jihar Bauchi sun cimma matsayar korar shugaban jam’iyyar na jihar Bauchi, Alhaji Babayo Aliyu Misau biyo bayan yanke tsammani ga salon jagorancinsa.
Bayan da suka sallami shugaban, sun kuma amince da naɗa mataimakinsa, Alhaji Muhammad Hassan Tilde a matsayin shugaban riƙon ƙwarya.
- Tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Henry Kissinger, Ya Mutu Yana Da Shekaru 100
- Gwamnatin Kaduna Ta Kaddamar Da Kwamitin Mutum 8 Don Inganta Harkokin Aikin Hajjin 2024
Shugabannin jam’iyyar waɗanda suka cimma wannan matsayar a zaman da suka gudanar a ranar Alhamis, inda suka ce, gaza iya shugabanci na Aliyu Misau ta sanya har jama’an jihar sun fara yanke ƙauna daga jam’iyyar don haka dole su ɗauki matakin kiyaye martabar jam’iyyar.
Da ya ke karanta wa ‘yan jarida matsayar shugabannin, mai bai wa jam’iyyar APC shawara kan harkokin Shari’a a jihar Bauchi, Barista Rabiu Garba, ya ce, bisa rashin iya shugabancin Babayo Aliyu Misau, jam’iyyar tana rasa tasirinta.
Ya ce, tun rikice-rikicen da aka samu a lokacin zaɓen cikin gida na jam’iyyar sun samu asali ne daga rashin iya shugabancin Misau, don haka suka yanke tsammani daga gareshi tare da cire shi baki ɗaya.
Barista Garba ta ce, “Biyo bayan zaman da shugabannin jam’iyyar APC a matakin jihar Bauchi suka yi, kamar yadda kuke gani, a cikin shugabanni 37, muna da mutum 27 da muka cimma matsaya guda, mun cimma matsaya, kowa ya amince tare da sanya hannu kan takara inda muka sauƙe tare da yanke tsammani daga shugabancin Alhaji Babayo Aliyu Misau a matsayin shugaban jam’iyyar APC a jihar Bauchi.
“Dalili kuwa, saboda gazawa da ya yi na yin jagorancin jam’iyya kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyya ya tsara. Kuma mun gaya masa a lokuta daban-daban ya gyara, ya ɗauki alƙawarin zai gyara amma har zuwa yanzu bai gyara ba.
“Kuma mun zo muka ga an kai wani matakin da ‘yan jihar Bauchi da shugabanninmu da zaɓaɓɓu da manyan shugabanninmu sun yanke tsammani daga shugabancinsa, kusan babu wanda yake goyon bayansa saboda an san ba zai kaimu ga gaci ba.
“Don haka muka ga dole mu yi wa kanmu ƙiyamullaili muka kira wannan zaman a yau domin amincewa da sauƙe shi.
“Mun yi amfani da sashi 17 (5) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ta 2022 (da aka yi wa kwaskwarima) muka sauƙe Alh. Babayo Aliyu Misau a matsayin shugaba.
“Sannan ƙarƙashin sashi 17 (6) na kundin tsarin jam’iyyar muka naɗa mataimakinsa Alh. Mohammed Hassan Tilde a matsayin shugaban jam’iyyar APC na jihar Bauchi na riƙon kwarya.
“Kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ta tsara, za mu rubuta wannan abun a rubuce za mu kai wa uwar jam’iyyar APC a Abuja za mu kai wa shugaban APC na ƙasa mu shaida masa abun da muka cimma.”
Kazalika, ya ce, bisa rashin iya jagorancin na Misau, jam’iyyar ta rasa kujeru da yawa a zaɓen 2023, kuma dole su ɗauki matakan da suka dace na farfaɗo da martabar jam’iyyar.
Kan shari’unsu da suke kotuna kuwa, Rabiu ya nuna cewa wannan sallamar na Misau ba zai shafi harƙoƙin Shari’a da jam’iyyar take yi ba, ya nuna kwarin guiwar cewa za su samu nasarori a shari’unsu da ke ake kan yi.
Da ya ke jawabin amsar mulki, shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyyar, Alhaji Muhammad Hassan Tilde, ya yi alƙawarin gudanar da shugabanci na kwarai tare da haɗa kan mambobin jam’iyyar a dukkanin matakai.
Ya nemi goyon bayan mambobi da shugabannin jam’iyyar domin ci gaban jam’iyyar da jihar Bauchi baki ɗaya.