Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron karawa juna sani kan zurfafa hadin kai da raya yankin kogin Yangtze Delta wato biranen gabobin kogin mashigar teku a Shanghai, inda ya gabatar da muhimmin jawabi. Ya ce, a cikin shekaru biyar da aka gabatar da shirin raya yankin kogin Yangtze Delta, gaba daya karfi da inganci na yankin sun ci gaba da zama a kan gaba a kasar. Ya jadadda cewa, yana da matukar muhimmanci ga kasar Sin ta gina wani sabon tsarin ci gaba, da sa kaimi ga bunkasuwa mai inganci, da gina kasa mafi karfi, da sake farfado da kasar ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin, don kara sa kaimi ga ci gaban yankin, da kara inganta fasahar kirkire-kirkire, gasa a fannin masana’antu, da matakin ci gaba, da yin jagoranci wajen samar da wani sabon salo na yin gyare-gyare da bude kofa ga babban mataki.
Xi ya gudanar da wannan taron tattaunawa ne a lokacin da yake gudanar da bincike a birnin Shanghai. Ya jaddada cewa, ya kamata yankin ya karfafa hadin gwiwar biranen a kan kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha, da kirkire-kirkire na masana’antu, da hanzarta inganta tsarin ci gaba, da inganta babban matakin hadin gwiwar bude kofa, da karfafa kiyaye da gudanar da harkokin muhalli tare, da kuma mai da hankali kan habaka karfin ci gaba mai aminci. (Mai fassara: Muhammed Yahaya)