Masu iya magana na cewa,abin da ya ci Doma bai barin Awai: Harin da ‘yan Bindiga suka kai gami da sace mutane a yankin Masarautar Dan Sadau, sakamakon kin biyan kudin fansa Naira miliyan 120, na kada hantar mutanan sauran kauyukan a koda yaushe sakamakon kin biyan nasu kudin.
Kauyukan da aka sanya wa kudin fansar aikin gona suna da dama amma,a Kananan Hukumomin Maru, Shinkafa, Anka, Maradun,Tsafe da Kauran Namoda abin ya fi tsanani.
- Majalisa Na Fuskantar Kalubalen Amincewa Da Kasafin Naira Tiriliyan 27.5 Na 2024
- Basirar Henry Kissinger Abu Mai Daraja Ne Ga Amurka
Domin ko a yanzu haka ‘yan Bindiga su kai hari a garin Ruwan Dorawa a mako biyu da suka wuce, inda suka sace mutum 13, da kisan mutum daya, sai kuma a ranar Juma’ar da ta gabata suka shiga yankin Masarautar Dan Sadau su kai sace mutum sama 100 a cikin daren wayewar gari Asabar da ta gabata.
Halin da da mutane Kauyukan, Mutunji, Kwanar Dutsi, Sabon Garin Mahuta da Unguwar Kawo, suke ciki baya ga sace mutanensu sama da 150 da ‘yan Bindigar suka yi karkashin jagorancin shugaban ‘yan Bindiga na Yanki Masarautar Dan Sadau Damuna.
Ya zuwa yanzu dai sama da mutane da dama ne suka dawo gidajansu sakamakon lokacin da ‘yan Bindiga suke tafiya da su suka fashe suka fantsama cikin daji.
Wannan ne ya yi sanadiyyar dawowar mutane da dama bayan kwana biyu da kai masu harin, amma har yanzu wasu na hannunsu wadanda ba a san adadin su ba.
Daya daga cikin wadanda ya kubuta daga hannun ‘yan bindigar da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa wakilinmu cewa, “A lokacin da ‘yan bindiga suka kora mu daji cikin dare da yake mun san yadda dajin yake da inda Dawa ke shuke da ciyayi masu tsawon duk inda aka a zo mutum ya san wurin sai ya sabe a guje ta haka ne mafi yawanmu muka tsira a hannun ‘yan Bindiga.”
“Ya kum tabbatar mana da cewa, shin Damuna zai sake dawowa garuruwan kuma lallai ba za su ji da dadiba.
Ana haka a ranar Lahadi sai ga motocin sojoji sun shigo garin amma zuwa Liitin sun bar garin, wannan ya kara sanya mana fargaba rashin sojoji a gari. Wannan ne ya sa yanzu haka wasu ke niyyar barin garin tun da ‘yan Bindiga sun tabbatar da cewa za su dawo kuma babu wani jami’in tsaro a garin.
A ta bangaren Gwamnatin Jihar Zamfara kuwa, ta bakin Gwamna Dauda Lawal da ya samu wakilcin, Shugaban Ma’aikata na Gidan Gwamnati, Muktat Muhammad Luga ya bayyana cewa, gwamnatin na sane da abubuwan rashin jindadi dake faruwa na tsaro a sasan jihar, gwamnatin na iyaka kokarinta don shawo kan matsalar tsaron.
Don yanzu haka ana ba wa ‘yan Sa kai horo domin tunkarar ‘yan Bindiga a duk inda suke a fadin Jihar.
Bangaren jama’an tsaro kuwa, Kakakin rundunar ‘yansandan na Jihar Zamfara, ASP Yazidu Abubakar ya bayyana wa manema labarai cewa, Rundunar Sojoji ne ke kula ya yankin Dan Sadau inda aka sace mutane sama mutum 100, sune ya kamata mu tuntuba.