Gwamnatin tarayya ta amince da kafa asusun tattara bayanai na ilimi, Ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a wani taro na wayar da kan masu ruwa da tsaki saboda saboda tsarin wanda aka yi a Abuja.
Mamman ya ce bayan amincewa da majalisar zartarwa ta kasa ta yi na gabatar da tsarin, bugu da kari ma ta amince da kafa sabon tsari domin ayyuka na tafiyar da sabon tsarin na ilimi.
- Har Yanzu Ƙanjamau Na Kashe Mutum Guda Duk Bayan Minti Ɗaya – Majalisar Ɗinkin Duniya
- Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Raya Yankin Delta Na Kogin Yangtze
Ya kara da cewa gabatar da tsarin NERD wani mataki ne da aka fara takawa a tarihi na al’amarin ilimi daya shafi makarantar data shafi Sakandare da kuma ta gaba da ita inda ya ce wani babban mataki ne mai amfani da gwamnatin tarayya ta dauka.
Ministan ya kara jaddada nan da shekaru biyar masu zuwa da gaba da su ma’aikatar ilimi ta tarayya tare da taimakon hukumar kulawa da jami’oi,hukumar al’amuran da suka shafi ilimin fasaha,hukumar kulawa al’amuran ilimin koyarwa, hukumar kula da dakin karatu ta kasa,da sauran masu fada aji ko ruwa da tsaki,sune za su yi jagorancin tsarin na NERD a matsayi na an kama hanya ta tafiya tare da zamani ta niyyar samun abubuwan da suka faru tun daga shekarar 1932 abin da ya shafi rahoto na ilimi da wanda aka wallafa a makarantunmu,wannan kuma ba tare da la’akari da wadanda suka mallake su ba ko masu zaman kansu ne ko na gwamnati,ko soja ko kuma farar hula.
“Wannan shi ne wani babban matakin da aka dauka na tara abubuwan ilimi na shekarun da suka gabata da kuma na yanzu za a samar da su, a manyan makarantun mu na jami’oi da wadanda suke mara masu baya,ba tare da samar da wata matsalar da zata shafi yadda suke tafiyar da al’amuran wasu nau’oin manyan makarantu ba musamman ma jami’oi.”
Karamin Minista ci gaban matasa Misata Ayodele Olawande,wanda shi ma yana daga cikins abon tsari ya jinjinawa ma’aikatar in da yace ita ranar “wata muhimmiyar rana ce a rayuwarsa”saboda ya kasance daga cikin wadanda suka gani da idon su yadda gwamnatin tarayya ta dauki mataki na wajen amfani da wani al’amari domin yin maganin babbar matsala da ke fuskanta ta tattara bayanai da suka shafi ilimi.
Shi ma a na shi jawabin maraba babban sakataren ma’aikatar Dabid Adejo ya bayyana cewa ma’aikatar ta fara tsara yadda za a fara tafiyar a shekarar 2014,ta yi aiki da hukumar da jami’oi ta kasa NUC da kuma kwararrun da za su bullo da yadda cikakken tsarin zai kasance.
Adejo ya yi bayanin shi tsarin na asusun tara bayanaiu na ilimi “NERD wani babban hobbasa ne da gwamnatin tarayya ta yin a ajiye ko tara bayanai wani babban tsari ne ne da zai taimkawa ba sai ta bangaren ilimi kadai ba,har ma abin ya shafi al’amarin tsaro.
Ma’aikatar ilimi tana hada kai da masu zaman kansu wajen kafa wani asusu ko Banki na farko da za a rika tara bayanai da suka shafi ilimi,shi ne na farko da za a kafa a nahiyar Afirka wanda zai rika taimakawa tattalin arziki ta fasahar zamani.”
Sauran wadanda suka yi jawabi sun hada da mai bada shawara na musamman ga Shugaban kasa kan al’amuran da suka shafi tattalin arziki Dakta.Tope Fasua,wanda jinjinawa ma’aikatar kan yadda ta maida hankalinta al’amarin daya shafi ilimi,da zummar cimma bunkasar tattalin arziki ta fasahar zamani. Gwamnatin tarayya ta amince da kafa asusun tattara bayanai na ilimi, Ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a wani taro na wayar da kan masu ruwa da tsaki saboda saboda tsarin wanda aka yi a Abuja.
Mamman ya ce bayan amincewa da majalisar zartarwa ta kasa ta yi na gabatar da tsarin, bugu da kari ma ta amince da kafa sabon tsari domin ayyuka na tafiyar da sabon tsarin na ilimi.
Ya kara da cewa gabatar da tsarin NERD wani mataki ne da aka fara takawa a tarihi na al’amarin ilimi daya shafi makarantar data shafi Sakandare da kuma ta gaba da ita inda ya ce wani babban mataki ne mai amfani da gwamnatin tarayya ta dauka.
Ministan ya kara jaddada nan da shekaru biyar masu zuwa da gaba da su ma’aikatar ilimi ta tarayya tare da taimakon hukumar kulawa da jami’oi,hukumar al’amuran da suka shafi ilimin fasaha,hukumar kulawa al’amuran ilimin koyarwa, hukumar kula da dakin karatu ta kasa,da sauran masu fada aji ko ruwa da tsaki,sune za su yi jagorancin tsarin na NERD a matsayi na an kama hanya ta tafiya tare da zamani ta niyyar samun abubuwan da suka faru tun daga shekarar 1932 abin da ya shafi rahoto na ilimi da wanda aka wallafa a makarantunmu,wannan kuma ba tare da la’akari da wadanda suka mallake su ba ko masu zaman kansu ne ko na gwamnati,ko soja ko kuma farar hula.
“Wannan shi ne wani babban matakin da aka dauka na tara abubuwan ilimi na shekarun da suka gabata da kuma na yanzu za a samar da su, a manyan makarantun mu na jami’oi da wadanda suke mara masu baya,ba tare da samar da wata matsalar da zata shafi yadda suke tafiyar da al’amuran wasu nau’oin manyan makarantu ba musamman ma jami’oi.”
Karamin Minista ci gaban matasa Misata Ayodele Olawande,wanda shi ma yana daga cikins abon tsari ya jinjinawa ma’aikatar in da yace ita ranar “wata muhimmiyar rana ce a rayuwarsa”saboda ya kasance daga cikin wadanda suka gani da idon su yadda gwamnatin tarayya ta dauki mataki na wajen amfani da wani al’amari domin yin maganin babbar matsala da ke fuskanta ta tattara bayanai da suka shafi ilimi.
Shi ma a na shi jawabin maraba babban sakataren ma’aikatar Dabid Adejo ya bayyana cewa ma’aikatar ta fara tsara yadda za a fara tafiyar a shekarar 2014,ta yi aiki da hukumar da jami’oi ta kasa NUC da kuma kwararrun da za su bullo da yadda cikakken tsarin zai kasance.
Adejo ya yi bayanin shi tsarin na asusun tara bayanaiu na ilimi “NERD wani babban hobbasa ne da gwamnatin tarayya ta yin a ajiye ko tara bayanai wani babban tsari ne ne da zai taimkawa ba sai ta bangaren ilimi kadai ba,har ma abin ya shafi al’amarin tsaro.
Ma’aikatar ilimi tana hada kai da masu zaman kansu wajen kafa wani asusu ko Banki na farko da za a rika tara bayanai da suka shafi ilimi,shi ne na farko da za a kafa a nahiyar Afirka wanda zai rika taimakawa tattalin arziki ta fasahar zamani.”
Sauran wadanda suka yi jawabi sun hada da mai bada shawara na musamman ga Shugaban kasa kan al’amuran da suka shafi tattalin arziki Dakta.Tope Fasua,wanda jinjinawa ma’aikatar kan yadda ta maida hankalinta al’amarin daya shafi ilimi,da zummar cimma bunkasar tattalin arziki ta fasahar zamani.