Idan ba a manta ba, a ‘yan makwannin baya; wannan shafi ya kawo muku wasu daga cikin amfanin da namijin goro ke da shi. Sai dai kuma a wannan makon, mun samu wani sabon bayani daga likita kan amfani da rashim amfanin namijin goro.
Kamar yadda likita ya yi bayani, muddin aka jima ana amfani da namijin goro; hakan na iya yin barazana ga kwayoyin halittar da suke taimakawa wajen haihuwa. Ma’ana, rashin samun haihuwa. Mutane da dama na amfani da namijin goro tare da sanya wa a ransu cewa, sakamakon sinadarin da namijin goron ke dauke da shi; zai iya taimaka wa maza wajen dandano ko gamsar da iyalansu yayin saduwar aure.
- Kamfanonin Nijeriya Sun Kara Wa Ma’aikatansu Albashin Naira Tiriliyan 4.6 Cikin Wata 6 -NBS
- Basirar Henry Kissinger Abu Mai Daraja Ne Ga Amurka
A dukkanin binciken da suka fito sun tabbatar da cewa; sinadarin namijin goro, ba ya kara wa da namiji kuzari ko karfin sha’awa ko kuma maganin mazakuta. Hasali ma, dadewa ana yin ta’ammali ko cin namijin goron ba bisa ka’ida ba, kan iya haifar wa da namiji matsalar rashin haihuwa.
Haka nan, namijin goro yana dauke da sinadarin da ke taimakawa wajen narka abinci, ya kuma taimaka wa jikin mutum wajen fitar da kwayoyin cutar da jiki bai san su ba ko kuma wadanda za su iya lalata garkuwar jiki.
Sannan namijin goro, na da sinadarin da ke taimakawa wajen ganin jiki ya samu waraka a bangaren kumburi tare da rage yawan kitsen da ke tattare a jikin dan Adam ya kuma sa kitsen ya ragu ya yi daidai wadaida.
Namijin goro na dauke da sinadarin da ke maganin abubuwan da ke da alaka da Maleriya ko ciwon siga, wanda ka iya yin maganin zazzabin cizon sauro, inda a wani bangaren ma ake ganin kamar ya fi alfanu ga masu ciwon siga; ta hanyar daidaita sigan idan ya yi yawa.
Har ila yau, namijin goro na dauke da sinadarin da ke bunkasa garkuwar jiki, ma’ana yana da abin da ake kira a turance ‘antiodidant’. A takaice, namijin goro na dauke da sinadarin da zai iya tallafa wa jikin dan Adam, ya fitar da abin da ka’iya zama guba a jikinsa.
Kazalika, namijin goro yana taimaka wa garkuwar jikin dan Adam, musamman wajen bude kofofin huhu, hanyoyin iska; wanda dan Adam musamman mai fama da matsalar asma ko fitar da numfashi, kan iya samun waraka idan ya yi amfani da wannan shi.
Mun samo muku daga tattaunawar da BBC ta yi da Dakta Auwal Musa Umar.