A ranar Talata ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi karo na 28, wanda ya gudana a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Baya ga halartar taron, shugaban ya gana da Sarki Charles na Ingila, da shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, da shugabannin kasashe da dama.
- An Bayyana Rawar Da Kasar Sin Ta Taka Kan Sauyin Yanayi Yayin Taron COP28
- An Rufe Taron Fahimtar Sin Na shekarar 2023
Har ila yau, shugaba Tinubu ya shaida rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta kara kaimi tsakanin Nijeriya da Jamus domin inganta wutar lantarki a Nijeriya, ya kuma shirya wani babban taro tare da masu ruwa da tsaki da masu zuba jari kan kasuwanci a Nijeriya da shirin kaddamar da motocin bas amfani da wutar lantarki.
A ranar 29 ga watan Nuwamba, 2023, Tinubu ya bar Abuja zuwa Dubai domin halartar taron da ake sa ran kammalawa a ranar 12 ga watan Disamba, 2023.
Gwamnatin Tinubu ta sha suka kan wakilai 1,411 da Nijeriya ta tafi da su domin halartar taron, amma gwamnatin ta ce mutane 422 ne kawai ta tura domin halartar taron.