• English
  • Business News
Tuesday, October 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Na Ba Da Gudummawa Ta Fuskar Ingiza Zamanantar Da Duniya

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

Yayin da duniya ke ci gaba da fuskantar manyan kalubale daga sassa daban daban, masharhanta na ganin wannan lokaci ne da ya dace sassan kasa da kasa su kara azamar bullo da dabarun hadin gwiwa, na tsame duniya daga mawuyacin halin koma bayan tattalin arziki da zamantakewa da take ciki.

Kaza lika, lokaci ya yi da duniya za ta rungumi matakan wanzar da zaman lafiya, da samar da ci gaban bai daya, domin cin gajiyar dukkanin al’ummun kasa da kasa. Hakan ne kuma ya sa har kullum kasar Sin ke sahun gaba a wannan fage. Idan mun lura da matakan da Sin ke dauka na baiwa ci gaban duniya gudummawa, za mu gamsu cewa matakai ne masu fa’ida ta kyakkyawan tasiri, ta yadda har kullum Sin din ke aiki tukuru, kuma kafada da kafada da sauran sassan duniya, wajen ganin an cimma burin zamanantar da al’amura, da samar da ci gaba cikin lumana, da aiwatar da matakan hadin gwiwa na bai daya.

  • Wang Yi: Sin Da Angola Sun Kafa Misali Na Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa 
  • Xi Ya Gana Da Shugaban Hukumar Gudanarwar Turai Da Shugabar Kungiyar EU

Sanin kowa ne cewa, duniya gida ne guda na daukacin bil Adama, kuma wuri na cin gajiyar daukacin al’ummun kasashen duniya, don haka kamata ya yi sassan kasa da kasa su kara kokarin yin hadin gwiwa, wajen shawo kan kalubalen dake addabar duniya, su goyi bayan matakan bunkasa duniya na bai daya, da inganta moriyar jama’a baki daya.

Idan muka yi la’akari da ci gaban da kasar Sin ke samu ta fuskar zamanantar da kasa, da fadada bude kofa bisa babban matsayi, da ma yadda kasar ke kara azamar bunkasa ci gaba mai inganci, za mu fahimci sirrin dake cikin damammaki da kasar ke samarwa, wajen ingiza ci gaban duniya.

Tsarin zamanantar da kasa na Sin, yana ci gaba da ingiza bunkasar tattalin arzikin duniya, kuma sabanin makamantansa da ake aiwatarwa a yanukunan yammacin duniya, salon kasar Sin na bayar da damar samun ci gaban bai daya. Tuni kasar Sin ta cimma manyan nasarori a fannin yaki da fatara, da kyautata rayuwar al’ummarta. Bisa hakan, muna iya cewa, salon zamanantarwa na Sin ya dace da burin daukacin bil Adama na samun ingantacciyar rayuwa.

LABARAI MASU NASABA

Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin

Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya

Yayin da Sin ke shiga sabon mataki na ci gaba mai inganci, kofofin takara mai tsafta suna kara budewa, kuma tsarin kasar na bude kofa ga kowa, da ingiza ci gaban bai daya, da gudummawarta a fannin gina budadden tsarin tattalin arzikin duniya, kyakkyawan labari ne ga duniya da a yanzu ke fama da tafiyar hawainiya a fannin na tattalin arziki.

Fatan dai shi ne duniya ta kara fahimtar kasar Sin, a matsayinta na abokiyar tafiya, ba wai barazana ko abokiyar hamayyar ko wane bangare ba. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin

October 14, 2025
Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya
Daga Birnin Sin

Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya

October 14, 2025
Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata
Daga Birnin Sin

Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata

October 14, 2025
Next Post
Shettima Ya Ziyarci Wadanda Sojoji Suka Jefawa Bam A Kaduna

Shettima Ya Ziyarci Wadanda Sojoji Suka Jefawa Bam A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Kotu

Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta

October 14, 2025
Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin

Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin

October 14, 2025
Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya

Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya

October 14, 2025
Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo

Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo

October 14, 2025
Asuu

An Janye Wajibcin Samun Kiredit A Darasin Lissafi Ga Ɗaliban Fannin Zamantakewa Don Shiga Manyan Makarantu 

October 14, 2025
Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata

Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata

October 14, 2025
Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato

Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato

October 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

October 14, 2025
‘Yan Majalisa 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga PDP

PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai

October 14, 2025
An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

October 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.