Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana rashin bin ka’ida da kuma rashin hukunci su ne ya sa ‘yan Nijeriya ba su amince da jam’iyyun siyasa ba.
Shugaban majalisar dattawa, wanda sanata mai wakiltar Anambra ta tsakiya, Bictor Umeh, ya wakilta, ya yi jawabi a wani taron da cibiyar Kukah ta shirya a Abuja, inda ya jaddada cewa jam’iyyun siyasa sun taimaka wajen inganta manufofi da gudanar da mulkin Nijeriya.
- Majalisar Dokokin Nasarawa Ta Amince Da Kasafin N199.9bn Da Gwamna Sule Ya Gabatar
- Badakala: Majalisar Wakilai Ta Bayar Da Umurnin Cafke Gwamnan CBN, Babban Akanta Na Kasa Da Sauransu
Ya ce jam’iyyun siyasa sun samar da hanyoyin da ‘yan Nijeriya za su bi don shiga cikin tsarin dimokuradiyya, yana mai cewa yana kira ga ‘yan Nijeriya kar su amince da abubuwan da suke gurbata dimokuradiyyar kasar nan.
“Wadannan batutuwa sun haifar da raguwar amincewar jama’a a cikin harkokin siyasar Nijeriya.
“Abin takaici ne ganin yadda ‘yan kasa ke nuna rashin jin dadinsu da wakilcinsu da kuma muradunsu na dimokuradiyya.”