Yawaitar hatsarin jiragen ruwa a fadin Kasar Nijeriya na da alaka da rashin bin dokoki tare da dibar kaya fiye da kima a jiragen ruwa da rashin yin amfani da rigunan kariya da rashin bin matakan kariya da rashin wadatattun kayan gyaran jiragen ruwa da kuma tafiye-tafiyen dare, hadi da kwasan fasinjoji fiye da karfin jirgin, kamar yadda binciken da jaridar LEADERSHIP ta tabbatar.
Kazalika, bayanan da LEADERSHIP ta samu daga sashin hakar ma’adinai na cewa, adadin mutum 911 da suka kunshi maza da mata da yara ne suka rasa rayukansu a hatsarin jiragen ruwa guda 61 da suka faru a tsakanin watan Junairun 2020 zuwa watan Nuwamban 2023.
- Matatar Dangote Ta Karbi Danyen Man Farko Da Za Ta Fara Tacewa
- Ya Kamata Kasashen Turai Su Kara Fahimtar Kasar Sin Don Karfafa Dangantakar Dake Tsakaninsu
Bayanan na nuni cewa, a tsawon shekaru shida da suka gabata, Nijeriya ta fuskaci hatsarin jiragen ruwa mafiya muni, inda rayukan mutum 1,204 suka salwatanta a tsakanin 2018 da Nuwamba 2023. A shekaru biyar da suka wuce, an samu rahotonnin afkuwar hatsarin kwale-kwale da rasa rayukan mutane da dama a jihohi 28 da ake iya bi ta hanyar ruwa a Nijeriya. Wadanda suka mutu sun hada da mata da yara, ko da yake an yi kokarin ceto wasu da dama a lokacin da suka gamu da hatsarin.
Rahotonni sun yi nuni da cewa a shekaru shida da suka gabata, sama da jihohi 12 ne aka samu rahotonnin mace-mace sakamakon hatsarin jiragen ruwa. Baya ga daruruwan mutanen da suka nutse suka baci a sakamakon hatsarin ruwa mafi muni da ake yawan samu a kasar nan.
A cewar rahoto, daga watan Janairun 2018 da Oktoba na 2023, an samu mutum 285 da suka mutu a Jihar Neja, Kebbi 144, Kwara 125, Sakkwato 117, Lagos 92, Anambra 80, Bauchi 76, Kano 45, Bayelsa 40, Taraba 50, Adamawa 60, sannan a Jihar Ondo da Benwai kuma aka samu mutum 34 da suka salwanta sakamakon wannan hatsarin.
A baya-bayan nan, an samu hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja a ranar Juma’a 16 ga watan Nuwamban 2023 da ya ci rayukan mutum 10.
A cewar rahotonni, jirgin ya gamu da hatsari ne a gundumar Gijiwa/Kato da ke Shiroro bayan da ya tashi daga Zangaro/Bassa/Kukoki dauke da fasinja sama da mutum 34 da suka hada da maza 20, mata 14.
Bugu kuma da kari, a watan Oktoban 2023, a kalla ‘yan kasuwan kauye 70 ne suka nutse a cikin ruwa yayin da wani kwale-kwale ya kife da su a Jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Nijeriya, kamar yadda jami’an hukumar agajin gaggawa suka shaida.
Kwale-kwalen da ya kwaso fasinjoji 100 da suka kunshi ‘yan kasuwa ciki har da yara, ya gamu da hatsari ne a gundumar Karim Lamido.
Shugaban shiyya na hukumar agajin gaggawa ta kasa NEMA, Ladan Ayuba, ya shaida cewa, “Ba a iya kirga mutum 73 ba daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su, an iya samun ciro gangar jikin mutum 17 zuwa yanzu. Daga cikin fasinjojin jirgin 104, mutum 14 an samu nasarar ceto su.”
Kazalika, kakakin hukumar samar da agajin gaggawa ta Jihar Taraba (SEMA), Bryson Ben, ya nakalto cewa mutum 18 ne aka samu rahoton mutuwarsu a hatsarin.
Har ila yau, labarin dai mai sosa zuciya, inda aka samu wani hatsari a Gbajibo da ke karamar hukumar Mokwa a Jihar Neja, inda fasinjoji sama da 100 ciki har da wadanda suke kan hanyarsu ta zuwa gonakai suka gamu da hatsarin kwale-kwale, lamarin ya ci rayukan mutum 24.
Wannan bala’in bai tsaya nan ba, inda a baya-bayan nan a Jihar Adamawa 15 daga cikin fasinjoji 23 sun rasa rayukansu a Njuwa Lake da ke karamar hukumar Yola ta kudu.
A shekarar 2021 an fi samun tashe-tashen hankula sakamakon hatsarin jiragen ruwa, musamman a yankin arewacin kasar nan. A Jihar Kebbi an samu wani mummunar hatsarin jirgin ruwa a watan Yuni da ya lakume rayukan mutum sama da 100, mafi yawansu ‘yan kasuwa ne da suke kan hanyarsu ta zuwa kasuwanci a Jihar Kebbi yayin da kwale-kwalen ya kife da su.
Kuma an sake samu wasu mutum 20 da suka rasa rayukansu a wani hatsarin ruwa a kogin Yauri dukka a jihar. Wadannan hatsare-hatsaren na bukatar dauka matakan gaggawa domin kyautata matakan kariya a tsarin sufurin hanyoyin ruwa.
Tashin hankalin da bacin rai kan rasa rayuka da ake yi, na ci gaba da faruwa, an samu wani hatsarin a Jihar Kano da ya ci rayukan mutum 29 ciki har da yara ‘yan makaranta da suke kan hanyarsu domin zuwa wani taron addini. Kari kuma da wasu yara bakwai da suka gamu da irin wannan matakin a Jihar Jigawa lokacin da kwale-kwale ya kife da su, dukka an gano cewa babu matakan kariya da ake bi wajen kiyaye afkuwar hakan.
Iyalai sun shiga dimuwa a Jihar Neja yayin da rayuka bakwai suka salwanta ciki har da yara a wani hatsarin jirgin ruwan a Zhigiri a watan Disamba. A Jihar Bayelsa mutum takwas suka mutu yayin da suke tafiya a kwale-kwale daga Ogboinbiri zuwa Amassoma.
A Jihar Ondo ma, ba ta tsira daga wannan mummunar ibtila’in ba, inda hukumar tsaro ta NSCDC ta ba da labarin cewa mutum hudu sun rasa rayukansu yayin da kuma wasu 19 suka jikkata a hatsarin kwale-kwale a watan Oktoba.
A watan Mayun 2021, hatsarin kwale-kwale a tsakanin jihohin Kebbi da Neja an rasa rayuka 70, yayin da mutum sama da 150 suka yi batan dabo.
A watan Oktoban 2022 a karamar hukumar Ogbaru da ke Jihar Anambra lokacin da kwale-kwale ya nutse cikin ruwa, ya janyo mutuwar mutum 76 daga cikin fasinjoji 85 da suke cikin jirgin. Mafiya yawansu kuma mata da yara ne a lokacin da suke kokarin yin hijira daga garuruwansu sakamakon ambaliyar ruwa.
A watan Mayun 2023, hatsarin kwale-kwale ya wakana a wani kogi da ke Jihar Sakkwato inda ya ci rayukan yara 15, yayin da kuma 25 suka nutse ba a iya samu su ba. A wannan watan a jihar da ke makwafta da ita wato Zamfara, mutum takwas suka salwanta a hatsarin kwale-kwalen da ya faru a Gusau.
Tashin hankali da bugun zuci bai karewa kan lamarn, inda a watan Yunin 2023 sama da mutum 106 suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwa a Patigi da ke Jihar Kwara. Kari a kan dalibai uku da suka rasa rayukansu a Kalaba ta Jihar Kurus Ribas.