Matatar Dangote ta tabbatar da cewa ta fara karbi danyen man fetur wanda za ta fara tacewa domin samar da man fetur da sauran abubuwan amfani.
Matatar ta Dangote za ta zama mafi girma a Afirka idan ta fara aiki.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Asibiti, Makaranta Da Gidaje Ga Al’ummar Tudun Biri – Gwamnan Kaduna
- Kasafin 2024: Tinubu Da Shettima Za Su Lakume Naira Biliyan 15.961Wajen Tafiye-tafiye
A cikin wata sanarwa, Aliko Dangote ya bayyana cewa wannan mataki ne mai muhimmanci.
Sanarwar ta ce matatar man fetur ta Dangote ta sayi gangar danyen mai miliyan daya daga wasu manyan kamfanonin hako danyen mai.
Ta ci gaba da cewa wani jirgin dakon kaya dauke da danyen man ya isa wurin sauke mai na Dangote, inda ya juye shi a cikin manyan rumbunan zuba danyen mai na matatar.
Kuma wannan, a cewar sanarwar shi ne kashin farko a cikin danyen mai ganga miliyan shida da matatar ta saye daga manyan kamfanonin hako danyen mai.
Kamfanin mai na Nijeriya (NNPC) ne ake sa ran zai samar da danyen fetur na gaba ga matatar, a cikin mako biyu zuwa uku masu zuwa, yayin da kamfanin ExxonMobil shi ma sai samar da wani bangare na danyen man fetur.
A watan Nuwamba ne NNPC ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar samar da danyen man fetur ga matatar.
Idan ba a manta ba gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari ce ta kaddamar da matatar man fetur ta Dangote kafin karewar wa’adinta.