An samu rashin zirga-zirgar ababen hawa a kan hanyar Gusau zuwa Dansadau mai matukar hadari a Jihar Zamfara, kamar yadda wata ziyarar gani ido da ta tabbatar.
Ziyarar dai na zuwa ne domin tabbatar da ko matafiya sun daina amfani da hanyar gaba daya sakamakon ci gaba da kai hare-hare, kashe-kashe, da garkuwa da fasinjoji da ‘yan fashin ke yi a yanzu haka da kuma rashin cin gajiyar hanyar saboda kara munana ayyukansu.
Hanyar mai nisan kilomita 110 na daya daga cikin hanyoyin gwamnatin tarayya a fadin kasar nan da ta lalace tare da haifar da wahalhalu masu tsanani da bakin ciki ga dimbin ‘yan Nijeriya.
- Ministan Wajen Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Mali
- Kasafin 2024: Tinubu Da Shettima Za Su Lakume Naira Biliyan 15.961Wajen Tafiye-tafiye
Arewa PUNCH ta nakalto cewa hanyar mai matukar muhimmanci ta dade a cikin wannan hali na na lalacewa duk da muhimmancinta na zirga-zirgar ta fuskar tattalin arziki, amma har yanzu ba a dauki matakai na gyara ta ba.
Titin da gwamnatin farar hula tun ta Jamhuriya ta biyu ta mulkin Tsohon Shugaban Kasa Shehu Shagari ta gina a shekarar 1982 ba a taba gyara ta ba tun daga wancan lokaci har zuwa shekarar 2002 lokacin da gwamnan farar hula na farko a Jihar Zamfara, Alhaji Ahmed Sani Yarima ya ba da kwangilar gyaran kananan hukumomin.
Akwai garuruwa da kauyuka da dama a kan hanyar Gusau zuwa Zamfara domin sama da kashi 30 cikin 100 na kayan abincin da jama’ar jihar ke nomawa mazauna wannan yanki ne suke samarwa.
Ziyarar da wakilinmu ya kai a titin ya nuna cewa gaba daya kwaltar ta lalace tamkar ba a taba yin ta ba gaba daya.
Majiya mai tushe ta shaida cewa kafin yanzu hanyar ta zama tarkon ajali sakamakon manyan ramuka, da dimbin ‘yan fashi da makami da ke jiran su ga mutane su yi garkuwa da su akan wannan hanya da ta taso daga Zamfara zuwa jihohin Kebbi da Kaduna.
Rahotanni sun ce an yi asarar rayuka da dama a kan hanyar gami da yin garkuwa da dubban mutane, kuma an biya miliyoyin Naira a matsayin kudin fansa ga masu garkuwa da mutane ta hanyar alaka da wadanda abin ya shafa, lamarin da ya tilasta wa al’ummar jihar daina bi ta hanyar in dai ba tare da rakiyar jami’an tsaron soji ba.
Wani mazaunin yankin mai suna Musa Garba ya shaida cewa dole ne masu ababen hawa da ke son tafiya kan titin su rika tafiya a kungiyance bayan sun samu amincewar jami’an soji na yi musu rakiya a ayarin motocin.
Garba ya ci gaba da bayanin cewa, yawan masu ababen hawa da za su bi wannan hanya mai hatsarin yawanci daga 20 zuwa sama ne wadanda dole ne su tafi da ayarin motocin da ke karkashin tsauraran matakai na rakiyar sojoji da ba su wuce 30 ba da za su ba su kariya idan ‘yan fashi sun yi kokarin kai musu farmaki.
Ya nanata cewa zai zama kamar wanu kunar bakin wake ne a ce direbobi ko da sun kai biyar ne in suka kuskura suka bi wannan hanya ba tare da rakiyar sojoji ba saboda ’yan fashin sun mamaye yankin baki daya.
A cewarsa, “Zai zama babban ganganci da jawo wa kai bala’i da kisan kai ga duk wanda ya yi yunkurin zuwa garin Dansadau daga Gusau ba tare da jami’an tsaro sun yi masa rakiya ba.
“Yankin wuri ne mai hadari, kuma babu wanda ya taba yunkurin zuwa Dansadau ba tare da jami’an tsaro ba.