Gwamnonin sojan Mali da Nijar sun bayyana shirin kawo karshen yarjejeniyar harajin da suka shafe shekaru da dama suna yi da Faransa cikin watanni uku masu zuwa.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da mahukuntan kasashen biyu suka fitar sun bayyana cewa, sun kawo karshen yarjejeniyar harajin ne saboda yadda Faransa ke ci gaba da nuna kyama ga kasashensu da kuma rashin daidaiton wadannan yarjejeniyoyin da ke haifar da asarar kudaden shiga ga kasar Mali da Nijar”, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran AFP ya ruwaito.
- Amfani Da Fahasa Zai Bunkasa Harkokin Zabe –Agu
- TGI Group Za Ta Hada Kai Da ABU Domin Bunkasa Kirkire-kirkire
Yarjejeniyar haraji ta Mali da Faransa ta kasance tun shekarar 1972, yayin da Nijar ta kulla yarjejeniya da kasar Turai tun shekara ta 1965.
An kirkiri dukkan yarjejeniyoyin biyu don hana haraji ninki biyu da saukake hadin gwiwa a cikin lamuran kudi.
Matakin dai ya biyo bayan irin wannan mataki da gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta dauka a farkon wannan shekarar.
Wannan dai shi ne mataki na baya-bayan nan a jerin matakan da gwamnatocin sojan kasashen uku suka dauka na yanke hulda da Faransa, wadda ke da karfin ikonsu, tun bayan da suka karbi mulki a juyin mulkin baya-bayan nan.